Gwamnan Jihar Plateau Caleb Mutfwang Ya Nada Mikel Obi Mai Ba Shi Shawara Na Musamman

Gwamnan Jihar Plateau Caleb Mutfwang Ya Nada Mikel Obi Mai Ba Shi Shawara Na Musamman

  • Gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang, ya ba shahararren tsohon dan wasan tsakiyar nan na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Mikel Obi mukami
  • Gwamna Caleb ya nada Obi matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin wasanni a gwamnatinsa
  • Gwamnan ya kuma sanar da karin wasu nade-nade da dama na mutanen da za su taimaka masa wajen tafiyar da gwamnatinsa

Jos, jihar Filato - Gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang ya sanar da nadin dan wasan kwallon kafan tsakiya na kungiyar Chelsea, John Mikel Obi a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin wasanni.

Sanarwar nadin na Mikel Obi na kunshe ne a cikin wani jawabin gwamnan da Daraktan yada labaransa Gyang Bere ya gabatar kamar yadda Daily Post ta wallafa.

An bai wa Mikel Obi babban mukami
Gwamna Caleb na jihar FIlato ya nada Mikel Obi mai ba shi shawara na musamman kan harkokin wasanni. Hoto: Mikel John Obi
Asali: Facebook

Takaitaccen bayani dangane da Mikel Obi

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani Ya Sadaukar Da Kashi 50 Na Albashinsa Don Hidimtawa Talakawan Kaduna

An dai haifi shahararren dan wasan kwallon kafa Mikel Obi, mai shekaru 36 a garin Jos, babban birnin jihar Filato.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kafin zuwansa Chelsea, Obi ya fara buga wasan kwallonsa ne a kulob din Plateau United, kafin daga bisani ya koma wani kulob din a kasar Norwey a shekarar 2004, lokacin yana dan shekara 17.

Obi ya shafe shekaru 14 yana bugawa Najeriya wasanni, ya kuma samu nasarori da dama, wacce daga ciki akwai kofin kasashen Afrika da ya ciyowa Najeriya.

Mike Obi ya bugawa Najeriya wasanni 91, wanda a cikinsu kuma ya zura kwallaye shida a raga.

Karin wasu mukaman da gwamna Muftwang ya ba da a jihar Filato

Gwamnan Caleb Mutfwang ya amince da nadin tsohon dan wasan tsakiyar ne da ma wasu sauran mutane domin su taimaka masa wajen gudanar da harkokin shugabanci a jihar.

Kara karanta wannan

An Samu Gwamnan APC Ya Yi Magana Game da Ministocin da Tinubu Ya Dauko

Daga cikin mukaman da gwamnan ya raba baya ga na Mikel Obi, akwai na bangaren kula da harkar malaman makarantun jihar TSC da SUBEB kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa.

Haka nan kuma akwai mukamin shugabancin Hukumar kula da lafiya ta jihar Filato (PLASCHEMA) da kuma na asibitin kwararru na jihar da gwamnan ya ba da.

Akwai karin wasu mukaman shugabancin muhimman hukumomi da kuma masu ba da shawara na musamman da gwamna Muftwang ya na da a fadin jihar ta Filato.

Gwamna Mutfwang ya taya sabbin hafsoshin tsaro murnar mukaman da aka ba su

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto cewa gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya taya sababbin shugabannin tsaro murna kan mukaman da suka samu.

Gwamna Mutfwang ya ce yana da kyakkyawan yakini kan cewa sababbin shugabannin tsaron na da gogewa ta musamman da za su iya kawo karshen matsalolin tsaro da ake fama da su a jihar da ma kasa baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng