Hasashen Yadda Tinubu Zai Rabawa El-Rufai, Wike, Pate da Ragowar Ministoci Ofis

Hasashen Yadda Tinubu Zai Rabawa El-Rufai, Wike, Pate da Ragowar Ministoci Ofis

  • An dade ana ta surutai kan wadanda za su zama sababbin Ministoci a Najeriya a mulkin Bola Tinubu
  • Yanzu an kama hanyar birne wannan magana, jama’a sun karkata kuma ga yadda za a raba mukaman
  • Hasashe ya nuna mukaman da Ahmad Dangiwa Umar, Lateef Fagbemi (SAN) za su rike idan an tantance su

Abuja - Bayan sanar da wasu daga cikin wadanda za su zama Ministocin, Legit.ng Hausa ta fahimci an bar masu fashin baki da magoya baya da aiki.

A irin na shi hasashen, Tolu Ogunlesi wanda ya yi aiki a fadar shugaban Najeriya ya fara tunanin yadda Bola Ahmed Tinubu zai yi rabon kujerun nan.

Mutane da-dama su na tunanin Nyesom Wike zai zama Ministan ayyuka, musamman idan aka tuna da kokarin da ya yi da yake Gwamna.

Kara karanta wannan

Sunayen Ministoci: Jerin Iyayen Gida Masu Tasowa a Siyasance Da Ka Iya Zama Ministocin Tinubu

Minista
Hannatu Musawa za ta zama Ministar Bola Tinubu Hoto: @NasiruSaniZango
Asali: Twitter

Haka zalika akwai Farfesa Muhammad Ali Pate wanda ya yi watsi da babban aiki a Duniya, saboda ana tunanin shi zai zama babban Ministan lafiya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hasashen raba mukaman Ministoci

1. Nyesom Wike - Ministan ayyuka

2. Yusuf Maitama Tuggar - Ministan harkokin waje

3. Muhammad Ali Pate - Ministan kiwon lafiya

4. Lateef Fagbemi - Ministan shari’a

5. Hannatu Musawa - Ministar al’adu

6. Iman S. Ibrahim - Ministar jin kai da bada tallafi

7. Badaru Abubakar - Ministan gona

8. Ahmad Dangiwa Umar - Ministan gidaje

9. Olubunmi Tunji-Ojo - Ministan sadarwa

10. Beta Edu - Ministar harkokin mata

11. Wale Edun - Ministar tattalin arziki

12. Waheed Adelabu - Ministan tsare-tsaren kasafin kufi

13. Joseph Terlumun Utsev - Ministan harkokin ruwa

14. David Umahi - Ministan sufuri

15. Dele Alake - Ministan yada labarai/harkoki na musamman

16. Nasir El-Rufai - Ministan lantarki

17. Mohammed Idris - Ministan sadarwa

Kujerar karamin Minista

A na mu hasashen, wadanda za su zama kananan Ministoci su ne irinsu Doris Uzoka, Ekperikpe Ekpo, Nkiru Nkiru Onyejiocha sai Stella Okotete.

Ragowar wadanda ake sa ran su zama Ministocin sun kunshi Bello Mohammed Goronyo, Mohammed Idris, Joseph Utsev da Sanata John Enoh.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Jawo Yaron Tsohon Gwamna, Ya Samu Babbar Kujera a Rabon Mukami

Tsofaffin Gwamnoni sun yi dace

Kun ji labari cewa mutanen Badaru Abubakar, Ezenwo Nyesom Wike, David Umahi Nasir El Rufai su na murnar hango kujerar Ministocin tarayya.

Har tsohon Gwamnan Ebonyi, David Umahi wanda yanzu yana majalisar dattawa, ya samu shiga, amma an yi watsi da wasu tsofaffin Gwamnonin APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng