Bayan Janye Masa, Yar Takara Mace Ɗaya Tilo Ta Shiga Cikin Ministocin Tinubu
- A ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli, shugaba Tinubu ya aika sunayen ministocin da aka jima ana dako ga majalisar tarayya domin tantancewa
- Honorabul Uju Kennedy Ohaneye, mace ɗaya tilo da ta nemi tikitin shugaban ƙasa a inuwar APC ta shiga jerin ministocin shugaba Tinubu
- Sai dai Barista Ohaneye ta janye kuma ta sanar da mara wa tsohon gwamnan Legas din baya a zaben fidda ɗan takarar shugaban ƙasa na APC
FCT Abuja - Daga ƙarshe, Honorabul Uju Kennedy Ohaneye ta samu shiga cikin muƙarraban shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Ita ce mace ɗaya tilo da ta nemi tikitin takarar APC kuma ta janye wa Bola Ahmed Tinubu a babban taro na musamman na zaben ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC a 2022.
Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa Ohaneye ta shiga cikin waɗanda shugaban ƙasa Bola Tinubu ya naɗa a matsayin ministocinsa.
A ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli, 2023, majalisar dattawa ta bayyana sunayen mutane 28 da shugaba Tinubu ya aiko mata a matsayin waɗanda zai naɗa ministoci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Godswill Akpabio, tsohon gwamnan Akwa Ibom kuma shugaban majalisar dattawa ne ya karanta sunayen ministocin ɗaya bayan ɗaya ga abokan aikinsa.
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gabajabiamila ne ya kai sunayen ministocin ga majalisa yayin da suke tsaka da zaman yau.
Yadda yar takara mace ta janye wa Tinubu
Idan baku manta ba sai da Ohaneye ta hau kan mumbari a filin babban taron zaben fidda gwanin APC ta tiƙa rawa kafin daga bisani ta sanar da janye wa daga takara.
Tana ɗaya daga cikin 'yan takara 7 da suka hakura suka janye wa mai nasara, shugaba Tinubu a wurin gangamin APC wanda ya gudana a filin Eagle Square.
Kafin ta sanar da janye wa daga tsaren da mara wa Tinubu baya, Ohaneye ta bada nishaɗi sosai a kan dandamali inda ta nuna salo daban-daban na rawa, Vanguard ta ruwaito.
Tsohon Gwamnan Ebonyi, David Umahi, Zai Yi Murabus Daga Kujerar Sanata
A wani labarin kuma Mataimakin jagoran majalisar dattawa, Sanata Dave Umahi, ya fara shirye-shiryen aje muƙaminsa a majalisar tarayya.
Umahi, tsohon gwamnan jihar Ebonyi ya fara yunkurin sauka daga matsayin sanata ne sakamakon naɗin da aka masa na Minista karkashin mulkin Bola Tinubu
Asali: Legit.ng