Shugaba Tinubu: Jihohin Mutane 28 Da Shugaba Tinubu Ya Nada Ministoci Sun Bayyana

Shugaba Tinubu: Jihohin Mutane 28 Da Shugaba Tinubu Ya Nada Ministoci Sun Bayyana

  • Daga ƙarshe, sunayen ministocin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da aka jima ana jira sun isa majalisar dattawan Najeriya
  • Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta sunayen ministoci 28 da Tinubu ya aiko domin tantance su a zauren majalisar ranar Alhamis
  • Shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ne ya kai sunayen ministocin yayin da Sanatoci ke tsaka da zamansu na yau

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Bayan tsawon lokaci, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana sunayen ministocinsa, lamarin ya ƙayatar da yan Najeriya da dama a sassan ƙasar nan.

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta sunayen ministocin a zaman sanatoci na yau Alhamis, 27 ga watan Yuli, 2023, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu: Jihohin Mutane 28da Shugaba Tinubu Ya Nada Ministoci Sun Bayyana Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jerin jihohin da aka haifi ministoci 28 da shugaba Tinubu ya naɗa

Kara karanta wannan

Bayan Janye Masa Takara, Mace Ɗaya Tilo Da Ta Nemi Tikitin APC Ta Samu Babban Mulki a Gwamnatin Tinubu

Jaridar The Cable ta yi nazari kan sunayen ministocin da shugaban ƙasa ya aika majalisa kana ta haɗa kowane da asalin jihar da aka haife shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sashi na 147 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya 1999 da aka yi wa garambawul ya tanadi cewa, "Ya kamata shugaban kasa ya naɗa akalla minista ɗaya daga kowace jiha, ya kasance haifaffen wannan jiha."

A tarihi, an samu saɓani a lokuta da dama kan adadin ministocin da ya dace kowace jiha ta samu, amma kundin tsarin mulkin ya ambaci cewa "aƙalla guda ɗaya daga kowace jiha."

Bisa la'akari da wannan tanadi, mun tattaro muku jerin sunayen ministocin da kuma jihohinsu, ga su kamar haka;

1. Abubakar Momoh (Edo)

2. Yusuf Maitama Tuggar (Bauchi)

3. Ahmad Dangiwa (Katsina)

4. Hanatu Musawa (Katsina)

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Sanatan APC Na Shirin Murabus Daga Majalisar Dattawa, Sahihan Bayanai Sun Fito

5. Uche Nnaji (Enugu)

6. Betta Edu (Cross River)

7. Doris Uzoka (Imo)

8. David Umahi (Ebonyi)

9. Nyesom Wike (Rivers)

10. Mohamed Badaru (Jigawa)

11. Nasir El-Rufai (Kaduna)

12. Ekperikpe Ekpo (Akwa Ibom)

13. Nkiru Onyejiocha (Abia)

14. Olubunmi Tunji-Ojo (Ondo)

15. Stella Okotete (Delta)

16. Uju Ohaneye (Anambra)

17. Bello Mohammed Goronyo (Sokoto)

18. Dele Alake (Ekiti)

19. Lateef Fagbemi (Kwara)

20. Mohammed Idris (Niger)

21. Olawale Edun (Ogun)

22. Adebayo Adelabu (Oyo)

23. Imaan Sulaiman-Ibrahim (Nasarawa)

24. Ali Pate (Bauchi)

25. Joseph Utsev (Benue)

26. Abubakar Kyari (Borno)

27. John Enoh (Cross River)

28. Sani Abubakar Danladi (Taraba)

Jerin Johohi 16 da Suka Gagara Fitar Da Sunayen Kwamishinoni Ana Saura Kwana 1 Wa’adi Ya Cika

A wani rahoton kuma Mun tattaro muku jerin jihohin da har yanzu ba su naɗa ministoci ba yayin da ya rage awanni 24 wa'adin doka ya cika.

Kara karanta wannan

Kace-Nace Yayin Da 'Yan Najeriya Suka Soki Yadda Tinubu Ya Zabi Ministoci, Sun Bayyana Abin Da Ya Kamata

Yayin da wasu jihohi suka tura sunayen kwamishinoninsu, akwai wadanda har yanzu babu alamun naɗa kwamishinoni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262