Jerin Johohi 16 da Suka Gagara Fitar Da Sunayen Kwamishinoni Ana Saura Kwana 1 Wa’adi Ya Cika

Jerin Johohi 16 da Suka Gagara Fitar Da Sunayen Kwamishinoni Ana Saura Kwana 1 Wa’adi Ya Cika

  • ‘Yan Najeriya na ci gaba da dakon ganin jerin sunayen ministocin Shugaba Tinubu tun bayan rantsar da shugaban
  • A dokar kasa, shugaban kasa da gwamnoni su na da kwanaki 60 ne kacal bayan rantsar da su don tura sunayen zuwa majalisa
  • Yau, 27 ga watan Yuli, saura kwana daya tak ga shugaban kasa da kuma gwamnonin wa’adin tura sunayen ya kare

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja – A dokar kasa, zababben shugaban kasa da kuma gwamnonin jihohin suna da kwanaki 60 kacal don nada ministoci da kwamishinoni bayan darewa mulki.

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari shi ya rattaba hannu a wannan doka a watan Maris da ta gabata, Legit.ng ta tattaro.

Tinubu Da Jerin Johohi 16 da Suka Gagara Fitar Da Sunayen Kwamishinoni Ana Saura Kwana 1 Wa’adi Ya Cika
Shugaba Tinubu Ya Gagara Fitar Da Jerin Sunayen Ministoci Don Tantancewa A Majalisa. Hoto: Information Nigeria.

Kamar yadda kundin tsarin mulki ya tabbatar, nada minista da kwamishinoni tare da tura sunayensu zuwa majalisa don tantancewa dole a aiwatar a cikin kwanaki 60 bayan rantsuwar kama mulki.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamna Aliyu Ya Miƙa Sunayen Sabbin Kwamishinoni 16 Ga Majalisar Dokoki

Saura kwana daya tak wa’adin ya kare ga Tinubu da gwamnoni

Shugaba Bola Tinubu da sauran gwamnoni sun yi rantsuwar kama aiki a ranar 29 ga watan Mayu na wannan shekara, TheCable ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya rage saura kwana daya kenan wannan wa’adi ya kare, yayin da rahotanni suka tabbatar cewa jerin sunayen ministocin Tinubu sun isa zuwa majalisar.

Yayin da wasu jihohi suka tura sunayen kwamishinoninsu, akwai wadanda ko alama babu na tabbatar da bin wannan doka, cewar Politics Nigeria.

Daga cikin jihohi 28 da aka fafata da su a zaben da aka gudanar a watan Maris, jihohi 12 ne kadai aka ruwaito cewa sun mika sunayen kwamishinoninsu zuwa majalisar dokokin jihohinsu.

Jihohin da suka mika sunayen kwamishinonin sun hada da:

1. Abia

2. Akwa Ibom

3. Bauchi

4. Ebonyi

5. Delta

Kara karanta wannan

Kace-Nace Yayin Da 'Yan Najeriya Suka Soki Yadda Tinubu Ya Zabi Ministoci, Sun Bayyana Abin Da Ya Kamata

6. Jigawa

7. Katsina

8. Kaduna

9. Kano

10. Rivers

11. Oyo

12. Taraba

Jihohin da suka gagara tura sunayen ministocinsu akwai:

1. Sokoto

2. Enugu

3. Cross River

4. Plateau

5. Niger

6. Lagos

7. Ogun

8. Kwara

9. Borno

10. Adamawa

11. Nasarawa

12. Kebbi

13. Benue

14. Zamfara

15. Yobe

16. Gombe

Har ila yau, Hukumar zabe ta kasa ta saka ranar da za a gudanar da zaben gwamnan jihohin Bayelsa da Imo da Kogi a ranar 11 ga watan Nuwamba.

Wike, Oyetola Da Sauran Sunayen Da Ke Cikin Ministocin Tinubu

A wani labarin, ana hasashen tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike da takwaransa na Kaduna Nasir El-Rufai na daga cikin ministocin Tinubu.

Ana ta dakon jiran jerin sunayen ministocin na Tinubu tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.

A yau 27 ga watan Mayu, saura kwana daya tak wa'adin da dokar kasa ta bayar akan nadin ministocin ya kare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.