Matsalolin Najeriya: Allah Na Fushi Da Mu, Dole Ba Za Mu Ga Da Kyau Ba, Tsohuwar Mataimakiyar Gwamnan Legas

Matsalolin Najeriya: Allah Na Fushi Da Mu, Dole Ba Za Mu Ga Da Kyau Ba, Tsohuwar Mataimakiyar Gwamnan Legas

  • Tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar Legas, Alhaja Sinatu Ojikutu, ta bayyana cewa fushin Allah ne ya sa 'yan Najeriya ke shan wahala
  • Ta ce zalunci, cin hanci da kuma mugunta sun yi katutu a zukatan da yawa daga 'yan Najeriya
  • Ta kuma bayyana cewa tsare-tsare da dokokin da gwamnati ta zo da su ne suke sanya 'yan Najeriya da yawa aikata laifuka

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Legas - Tsohuwar zababbiyar mataimakiyar gwamna ta farko a Najeriya, Alhaja Sinatu Ojikutu, ta alakanta matsalolin Najeriya da fushin Ubangiji.

Ta ce 'yan Najeriya ba za su ga da kyau ba saboda karya, mugunta da kuma cin hanci da ya yi yawa a tsakanin 'yan kasar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Alhaja Sinatu ta ce Allah na fushi da 'yan Najeriya
Mataimakiyar gwamnan Legas ta farko ta ce fushin da Allah ke yi da 'yan Najeriya ne ya sa ake shan wahala. Hoto: Crown FM
Asali: UGC

'Yan Najeriya na bautar wasu ababen bautar da ba Allah ba

Ojikutu ta bayyana cewa ana bautar ababen bauta da yawa a Najeriya sabanin a bautawa Ubangiji na gaskiya shi kadai.

Kara karanta wannan

"Babu N8,000" Cikakken Jerin Garaɓasa 6 da FG Ke Shirin Raba Wa 'Yan Najeriya Don Rage Raɗaɗi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cikin wani jawabi da ta rabawa manema labarai ranar Alhamis a Legas, Ojikutu ta ce 'yan Najeriya ba sa son junansu, sai bakar mugunta ga junansu.

Ta kuma ce da gangan gwamnatoci ke kin biyan albashin ma'aikata saboda a cewarta, gwamnati tana da iassun kudaden biyan ma'aikata.

Dokokin gwamnati sun sanya mafi yawan 'yan Najeriya aikata laifuka

Ojikutu ta ce gwamnai ta samar da dokoki da tsare-tsare da suka mayar da kaso 99% na 'yan Najeriya masu aikata laifuka.

Ta ce kusan duk wani abu da mutum zai yi yanzu a Najeriya sai ya karya doka sannan zai yiwu.

Ta ba da misali da yadda mutane ke bugo takardun karatu na bogi da kuma yadda mutane ke sauya bayan na'urar auna wutar lantarki da ake sha a gidaje.

A wani bangare na kalamanta ta ce:

Kara karanta wannan

Kowa Zai Samu: Gwamnati Ta Bayyana Yadda Rabon N8000 Na Tinubu Zai Wakana

"Idan ka karanta littafi mai tsarki sannan ka duba abin da ke faruwa a Najeriya, zaka gane cewa Allah yana fushi da kasar nan."

A rahoton jaridar Nigerian Tribune, Ojikutu ta ce dukkan wasu matsaloli na tsadar rayuwa da ake fama da su, 'yan Najeriya ne suka janyowa kansu.

'Yan Najeriya sun rasa inda gwamnatin Tinubu ta dosa

Legit.ng a baya ta yi wani rahoto da ke bayyana yadda 'yan Najeriya ke kokawa kan rasa gane kan inda gwamnatin shugaba Tinubu ta dosa.

Mutane da dama sun koka bisa yadda sabbin tsare-tsaren gwamnatin ta Tinubu ke kara sanyasu cikin takura.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng