Tinubu Na Neman Kare Kansa Daga Sammacin Da Atiku Ya Yanko Masa a Kotun Amurka

Tinubu Na Neman Kare Kansa Daga Sammacin Da Atiku Ya Yanko Masa a Kotun Amurka

  • Shugaba Tinubu ya nemi a soke wani sammaci da Atiku ya yanko masa a wata kotu da ke ƙasar Amurka
  • Atiku ya nemi Tinubu ya gurfanar a gaban kotun da ke Illinois na jihar Chicago don amsa tambayoyi
  • Atiku na neman sanin duka bayanan karatun da Tinubu ke iƙirarin ya yi a jami'ar jihar Chicago da ke Amurka

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya shigar da buƙatar soke sammacin da Atiku ya yanko masa a gaban wata kotu da ke Illinois, jihar Chicago ta ƙasar Amurka.

A ranar 11 ga watan Yuli ne, Atiku ya shigar da ƙara yana neman samun ƙarin bayani kan bayanan karatun Tinubu a jami’ar jihar Chicago kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Tinubu ya nemi a soke ƙararsa da Atiku ya shigar a Amurka
Tinubu ya nemi a soke sammacin da Atiku ya yanko masa a Amurka. Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Atiku ya nemi cikakken bayani dangane da karatun Tinubu a jami'ar jihar Illinois

Kara karanta wannan

Mai Shari'a Ugo: Babban Alkalin Da Ke Jagorantar Shari'ar Neman a Soke Zaben Tinubu Ya Yi Murabus? Gaskiya Ta Bayyana

Daga cikin takardun da Atiku ya nema ta hannun lauyarsa, Angela M. Liu, akwai shaidar shigarsa jami'ar da ta ɗaukarsa, kwanakin da ya yi har zuwa lokacin da ya kammala digiri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan Atiku ya nemi sanin lambobin yabo da karramawa da Tinubu ya samu a lokacin da yake karatu a jami’ar da dai sauransu.

Atiku ya faɗawa kotun cewa, ya yanki takardar sammacin da aka aikawa Tinubu ne domin tabbatar da gaskiyar abubuwan da yake iƙirari.

Ya kuma shaidawa kotun cewa, yanzu haka Tinubu ne shugaban ƙasar Najeriya kuma yana fuskantar shari’a daban-daban da ke da alaƙa da zaɓensa da kuma sahihancin takardun karatunsa a jami’ar jihar Chicago.

Martanin Tinubu dangane da sammacin da Atiku ya yanko masa a Amurka

Da yake mayar da martani kan ƙarar, lauyan Tinubu, Victor P. Henderson a ranar 19 ga watan Yuli, ya buƙaci kotun da ta yi watsi da ƙarar saboda babu wani alƙalin kotun da ya saurari karar kuma ya ba Atiku sammacin.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima Ya Miƙa Wata Babbar Buƙata Ga Tsoffin Sanatoci Dangane Da Gwamnatin Tinubu

Ya yi iƙirarin cewa ƙarar ba ta inganta ba sakamakon kwanaki shida kacal da ake so wanda aka yi ƙarar ya bayyana gaban kotu, wanda bai kai kwanaki 14 na ƙa'ida ba kamar yadda yake a sashe na 219 da 137 na dokokin kotun ƙoli na Illinois.

Ya ƙara da cewa Atiku bai canko daidai ba wajen ƙoƙarin yankowa Tinubu sammaci a kotun ta Illinois kamar yadda rahoton na Daily Trust ya ƙara bayyanawa.

PDP ta yi hasashen abinda zai faru idan kotu ta tsige Bola Tinubu

legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto wanda jam'iyyar adawa ta PDP ta yi hasashen abinda zai faru a lokacin da kotu ta sanar da tsige Shugaba Tinubu.

PDP ta bayyana cewa 'yan Najeriya za su yi taka rawa su yi murna a kan titunan ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng