‘Yan NWC ba su Goyon Bayan Zaman Ganduje Sabon Shugaban Jam’iyyar APC
- Abdullahi Adamu da Iyiola Omisore sun jika aiki a APC da su ka yi murabus daga mukamansu
- Ana yawo da sunan Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda zai zama sabon shugaba na kasa
- Wasu shugabanni a jam’iyya mai-ci sun karyata maganar ko kuwa su nuna ba su goyon bayan haka
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Akwai alamu mai karfi da ke nuna wasu ‘yan majalisar gudanarwa ta NWC na jam’iyyar APC, ba su yi amanna da Abdullahi Umar Ganduje ba.
A rahoton Punch, an ji cewa maganar kawo Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda zai canji Abdullahi Adamu, bai kwantawa wasu a APC ba.
Daga cikin korafin da ake yi shi ne tsohon Gwamnan mai shekaru 73 ya fito daga jihar Kano ne, alhali Arewa maso tsakiya ta ke rike da shugabanci.
Yadda aka shawo kan Ganduje
Wata majiya da ke kusa da Abdullahi Ganduje wanda ya yi shekaru takwas yana Gwamna a Kano ta ce an dauko shi ne saboda biyayya da amanarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana ganin tsohon Gwamnan zai iya canza yadda abubuwa su ke tafiya a APC, ya ce Gwamnonin Imo da Kwara ne su ka roki Dr. Ganduje ya karbi kujerar.
A kan wannan batu, ba a iya samun Felix Morka domin jin ta bakinsa ba a matsayinsa na Sakataren yada labaran APC na kasa, bai amsa waya ba.
Duk jita-jita ce kurum ake yi
An rahoto Mataimakin shugaban APC a Kudu, Emma Eneukwu ya na cewa maganar nada tsohon Gwamnan ya zama shugaban jam’iyya rade-radi ne.
Eneukwu yake cewa jita-jita ce kurum ke yawo cewa Ganduje zai karbi shugabancin jam’iyyar APC, ya ce ba zai iya magana kan abin da bai tabbata ba.
Dr Ijeoma Arodiogbu shi ne shugaban APC na Kudu maso gabas ya ce sun yi zama a jiya, kuma babu inda aka kawo maganar ba Ganduje rikon jam’iyya.
Hon. Nze Chidi Duru mai rike da kujerar mataimakin sakataren gudanarwa yayi mamakin jin labari nan, amma bai iya cewa uffan a kan batun ba.
Abin da ya kamata APC tayi
Tsohon mai magana da yawun APC, Yekini Nabena ya ce za a san wanda zai zama sabon shugaban jam’iyya na kasa ne ta hanyar kada kuri’u a zabe.
Shi kuwa Garus Gololo wanda yana cikin manyan jam’iyya mai mulki, yana goyon Tanko Al-Makura, ya ce ba adalci ba ne a kai kujerar zuwa jihar Kano.
...Martanin Salihu Lukman
Ku na da labari wasu da ke rike da mukamai a jam’iyya ba su boye adawarsu ba. Daga cikinsu akwai Salihu Lukman mai wakiltar yankin da Ganduje ya fito.
Mataimakin shugaban jam’iyyar yana cikin masu ganin za ayi wa Arewa ta tsakiya rashi adalci. An koka da haka tun wajen zaben shugabannin majalisa.
Asali: Legit.ng