Gwamnan PDP Ya ba Kan Shi, Yaronsa da Surukarsa Matsayi a Mukaman da Ya Raba

Gwamnan PDP Ya ba Kan Shi, Yaronsa da Surukarsa Matsayi a Mukaman da Ya Raba

  • Yaron Marigayi Isiaka Adeleke ya na cikin wadanda Gwamnan jihar Osun ya ba mukami a makon nan
  • Shi ma Gwamnan zai rike Kwamishinan ayyuka, kuma ya jawo ‘yan tawaren APC ya ba su kujeru a Jihar
  • Akwai surukar Gwamnan da ta shiga cikin Kwamishinonin da aka nada bayan dogon lokaci ana jira

Osun - Ademola Adeleke ya nada yaron Marigayi Isiaka Adeleke a cikin shugabannin majalisun da ke sa ido a ma’aikatun gwamnatin jihar Osun.

The Nation ta ce Mai girma Gwamnan Osun ya ba Tunji Adeleke shugabancin majalisar da ke sa ido a aikin hukumar kula da kananan hukumomi.

Mista Tunji Adeleke wanda mahaifinsa, Isiaka Adeleke ya taba rike kujerar Gwamna a Osun, ya samu wannan mukami duk da a 2020 ya gama jami’a.

Gwamna
Gwamna Ademola Adeleke yana rawa Hoto: @AAdeleke_01
Asali: Twitter

Kwanakin baya aka yi ta surutu saboda Gwamnan ya zabi matar yayansa, Adenike Adeleke ta zama Kwamishina bayan shafe watanni bai nada ba.

Kara karanta wannan

An Yi Son Kai: Majalisa Za Ta Binciki Duka Mukaman da Aka Bada a Mulkin Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun Adeleke, Olawale Rasheed ya tabbatar da cewa an nada shugabanni da mataimakan majalisun hukumomin gwamnati 19.

Hukumomi, ma’aikatu da cibiyoyin sun hada da jami’ar jihar Osun, kwalejin ilmi ta Ola, kwalejin koyon aikin kiwon lafiya da ke Ilesha da hukumar SUBEB.

An zabi wadanda za su lura da hukumar jin dadin alhazai, hukumar yawon bude ido, hukumar tara haraji, asibitin koyon aiki da kuma hukumar inshora.

An kebewa Kwamishinoni wasu kujeru

A wani rahoton na Vanguard, an ji yadda Ademola Adeleke ya zabi kan shi a matsayin Kwamishinan ayyuka, bai ba kowa wannan ma’aikata ba.

Gwamnan ya kuma zabi Kola Olawusi wanda shi ne mataimakinsa, zai rike Kwamishinan wasa da harkoki na musamman a majalisar zartarwa.

Jaridar ta ce Gwamnan ya dauko wani lauya, Sola Akintola, ya ba shi Kwamishinan kiwon lafiya.

Kara karanta wannan

Yadda Zulum Ya Mamayi Ma’aikatan Lafiya, Ya Ziyarci Asibiti Cikin Tsakar Dare

'Yan adawar APC sun more

Shugaban APC na bangaren ‘yan taware a karkashin jagorancin Rauf Aregbesola, Razak Salinsile ya samu mukami a karkashin gwamnatin Adeleke.

Biyi Odunlade wanda ‘dan APC ne kuma ya na cikin na kusa da tsohon Ministan cikin gidan wanda ake rikici da su a jihar Osun, ya samu mukami.

'Dan shekara 29 ya zama Likitan Gwamna

Rahoto ya zo cewa Gwamnan Katsina ya dauko wani matashi Abdulrahim M. Ma’aji da ya yi karatu a kasar Sudan domin zama Likitan da ke duba shi.

An kafa jami’ar da ya yi karatu ta Ibn Sina ne a 2000 a birnin Khartoum, ta shahara musamman a shekarun baya-bayan nan a ilmin kiwon lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng