Shema da Tawagarsa Sun Ziyarci Gwamna Dikko Radda a Katsina

Shema da Tawagarsa Sun Ziyarci Gwamna Dikko Radda a Katsina

  • Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗda ya karɓi bakuncin tsohon gwamna, Ibrahim Shema a gidan gwamnatin Katsina
  • Shema tare da tawagarsa sun kai wa gwamna ziyara ne domin taya shi murna bisa rantsar da shi a matsayin gwamna cikin nasara
  • Gwamna Radda ya gode wa Shema bisa gudummuwar da ya bai wa APC har ta samu nasarar lashe zaɓe ranar 18 ga watan Maris

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Katsina state - Tsohon gwamnan jihar Katsina, Barista Ibrahim Shehu Shema ya ziyarci gwamna mai ci, Malam Dikko Umaru Raɗda, a gidan gwamnatin jiha da ke cikin birnin Katsina.

Barista Ibrahim Shema, ya rike kujerar gwamnan Katsina tsawon zango biyu daga shekarar 2007 zuwa 2015 ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP.

Ibrahim Shema tare da Malam Dikko Radɗa.
Shema da Tawagarsa Sun ziyarci Gwamna Dikko Radda A Katsina Hoto: @Miqdad_jnr
Asali: Twitter

Shema ya kai wa Dikko Raɗɗa ziyara tare da tawagarsa ranar Talata, 18 ga watan Yuli, 2023, inda suka tattauna kan wasu batutuwa.

Kara karanta wannan

Kano: Ganduje Ya Magantu Kan Batun Ciyo Bashin Biliyan 10 Don CCTV, Ya Fayyace Gaskiyar Al'amari

Mai taimaka wa gwamna Raɗɗa na musamman kan harkokin digital midiya, Isah Miqdad, shi ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Tuwita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene dalilin wannan ziyara da Shema ya kia wa Raɗɗa?

Sanarwan ta haƙaito Shema na cewa babban makasudin da ya jawo suka kai wa Raɗɗa ziyara shi ne su taya shi murna bisa nasarar cin zaɓe da kuma rantsar da shi a matsayin sabon gwamna.

A cewar Shema, jihar Katsina tana buƙatar mutane kamar Raɗɗa domin ci gaba kuma ya yaba da kamun ludayin sabon gwamnan.

Shema ya ce sabon gwamnan ya fara aikin da ya dace daga shiga Ofis bisa haka ya roƙi Raɗɗa da kar ya yi ƙasa a guiwa a aikin da ya ɗauko domin amfanar Katsinawa.

Gwamna Radɗa ya gode da ziyarar Shema

Kara karanta wannan

Jerin Takwarorin Shugaba Tinubu Gwamnonin 1999 Da Aka Taba Garkame Wa a Gidan Gyaran Hali

A nasa jawabin, Dikko Raɗɗa ya gode wa Shema bisa ziyarar da ya kawo masa da kuma goyon bayan da ya ba shi har Allah ya sa ya lashe zaɓen gwamna a watan Maris.

Duk da kasancewarsa mamban PDP, Barista Shema da jiga-jigan da ke mara masa baya sun goyi bayan Dikko Raɗɗa na jam'iyyar APC a zaben ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Shugaba Tinubu Ya Gana da Jonathan da Wasu Gwamnoni a Aso Villa

A wani labarin kuma Tsohon shugaban ƙasa, Dakta Goodluck Ebele Jonathan ya gana da shugaba Bola Ahmed Tinubu a Aso Villa da ke Abuja ranar Talata.

Wasu jiga-jigan gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki da suka haɗa da Hope Uzodinma na Imo da Abdulrahman na Kwara sun halarci taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel