Duniya Kenan: Tsohon Jigo Ya Tuno ‘Rigimarsa’ da Shugaban APC da Ya Sauka
- Daniel Bwala ya ce Abdullahi Adamu ne ya sha alwashin ba zai biya shi kudin aikin da ya yi wa APC ba
- A yau sai ga shi tsohon Gwamnan na Nasarawa ya sauka daga kujerar Shugaban jam’iyyar APC na kasa
- Lauyan ya yabi siyasar Yarbawa wadanda ya ce ba su dauki abin da zafi ba, akasin wasu mutanen Arewa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Daniel Bwala ya yi aiki da Atiku Abubakar wajen yakin neman zaben shugaban kasa a jam’iyyar PDP, ya tuno takaddamarsa da APC.
Da jin labarin Abdullahi Adamu ya sauka daga kujerar shugaban jam’iyyar APC na kasa, lauyan ya bada labarin yadda su ka yi da shi kan hakkinsa.
Bwala ya nuna Sanata Adamu ya isa ya zama darasi, a bayanin da ya yi a Twitter, ya yabi Yarbawa da cewa sun kware wajen siyasa ba tare da gaba ba.
Siyasa ba da gaba ba sai Yarbawa?
A duk lokacin da ya hadu da Shugaba Bola Tinubu da mutanensa, Bwala ya ce ana yin wasa ne da dariya tamkar bai bar jam’iyyar ta APC mai-ci ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Akwai ranar da Babatunde Oglala, SAN ya ci karo da jigon na PDP (a yanzu) a kotu, ya ce a gaban mutane ya fada masa dolensa ya dawo jam'iyyar APC.
Baya ga irin wannan raha, kwanakin baya ya ce sun yi wasa da dariya da Dr. Kayode Fayemi, amma ya rika yin baram-baram da jagororin APC na Arewa.
Amma a lokacin da ya yi kicibis da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a jirgin sama, babu abin da ya hada su tun daga Birtaniya illa sallama.
A sa’ilin ne masanin shari’ar ya ce su ka yi ta hira da shugaban majalisa, Femi Gbajabiamila.
Maganar Daniel Bwala a Twitter
“Amma ‘yanuwana na Arewa da ke APC sun daina yi mani magana saboda na bar jam’iyyar kuma wani daga cikinsu ya ki biya ni kudin aikin shari’a na.
Akwai daidaikun ‘yanuwana daga Arewa da sun fita dabam, kuma har yau mu na zumunci. Ubangiji ya nuna mana ikon gane siyasa ba gaba ba ce.
Domin shakka babu, mulki ba abin dorewa ba ne.”
Masoyi ya koma makiyi a APC
Kafin ya bar jam’iyyar APC mai mulki saboda an tsaida Bola Tinubu da Kashim Shettima, Daniel Bwala ya rike babban mukami a majalisar NWC.
Kafin zabe aka taba rahoto shi yana cewa satar da aka tafka a gwamnatin Shugaba Buhari ta dama wanda aka yi cikin shekaru 16 na gwamnatin PDP.
Asali: Legit.ng