Yarbawa Sun Fara Kuka da Tinubu Kan Yawan Fifita Legas Wajen Nada Mukamai
- ‘Yan 'South West APC Support Group' sun soma korafin rashin daidaito wajen rabon mukamai
- Shugaban kungiyar ya ce ‘Yan Legas ne su ka tashi da mafi yawan kujerun da Bola Tinubu ya raba
- Otunba Dele Fulani ya fitar da jawabi yana mai gargadin Bola Tinubu ya tuna da sauran Yarbawa
Lagos - Wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC a yankin Kudu maso gabashin Najeriya sun fito da wuri domin jan kunnen Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A rahoton da Leadership ta fitar, an ji cewa kungiyar SASG ta nusar da Mai girma shugaban kasa cewa mutanen Legas su ke tashi da kusan duk mukamai.
Wannan kungiya ta magoya bayan jam’iyyar APC a Kudu maso yamma ta ce ana ware sauran jihohin bangaren, ana fifita Legas inda Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban SASG ya na ganin yaran Legas su ka amfana da mafi yawan kujerun da aka raba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar SASG ta nuna damuwarta
Otunba Dele Fulani ya ce sun damu da yadda abubuwa su ke tafiya, kuma su na tsoron cigaba da irin hakan wajen nadin Ministoci da sauran ma’aikatu.
A cewar Otunba Dele Fulani, kungiyarsu ta lura cewa a cikin hadimai 20 da shugaban Najeriyan ya nada a kwanaki, akalla 13 daga cikinsu daga Legas su ke.
SASG ta ce muddin ba ayi gyara ba, Kudu maso yamma za a fara zalunta a mulkin nan, ta na mai fadawa ‘yan siyasar Legas su daina matsawa Tinubu lamba.
Ba Legas kadai su ka taimaki APC ba
Jawabin Otunba Fulani ya tunawa Shugaban irin gudumuwar da sauran jihohin Yarbawa su ka bada wajen ganin ya yi nasara a zaben da aka yi a bana.
Asali ma dai SASG ta sake tunatar da Mai girma Tinubu cewa jihohin Ondo, Ekiti da Oyo sun fi yi wa jam’iyyar APC kokari a zaben 2023 a kan jihar Legas.
Da aka tashi kafa kwamiti da zai yi aikin rabon mukamai a ma’aikatun tarayya, Femi Gbajabiamila aka ba shugabanci sai George Akume ya zama sakatarensa.
Ganin an dawo da tsohon Gwamnan Legas watau Akinwunmi Ambode, ana maganar za a ba shi Minista, SASG ta ce hakan ya gaskata tsoron da ta ke da shi.
Tallafin cire tallafin fetur
An rahoto Dele Alake yana cewa gwamnatinsu za ta sake duba tsarin raba kyautar N8, 000 domin kawo sa’ida ga marasa karfi ba tare da bata lokaci ba.
Gwamnatin tarayya za ta sanar da mutanen Najeriya daukacin tsarin tallafin da gwamnati ta ke da shi kuma za a fito da taki da hatsi domin a raba.
Asali: Legit.ng