Sakataren Jam'iyyar PDP Na Jihar Kwara Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa
- Sakataren jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na jihar Kwara ya yi murabus daga kan muƙaminsa na shugabanci a jam'iyyar
- Alhaji Rasaq Lawal ya kuma sanar da ficewarsa daga jam'iyyar ta PDP mai adawa a jihar ta Kwara bayan yin murabus ɗin nasa
- Tsohon sakataren ya bayyana cewa ya yanke hukuncin yin murabus da ficewa daga jam'iyyar ne saboda wasu dalilai na ƙashin kansa
Jihar Kwara - Sakataren jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ƙwara, Alhaji Rasaq Lawal, ya yi murabus daga muƙaminsa.
Jaridar Nigerian Tribune ta ce Lawal ya sanar da murabus ɗin nasa ne a cikin wata wasiƙa da da ya aikewa da shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Hon. Babatunde Mohammed a ranar Talata, 18 ga watan Yuli.
A cikin wata wasiƙa kuma da ya aikewa shugaban jam'iyyar PDP na mazaɓar Badari a ƙaramar hukumar Ilorin ta Yamma, Alhaji Lawal ya sanar da ficewarsa daga cikin jam'iyyar, rahoton New Telegraph ya tabbatar.
Yaƙar Tinubu Da Wasu Dalilau 4 Da Suka Sanya Abdullahi Adamu Yin Murabus Ɗin Dole Daga Shugabancin APC
Dalilin yin murabus ɗinsa da ficewa daga jam'iyyar PDP
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cikin wasiƙun da ya aike da su, Lawal ya bayyana cewa ya yanke hukuncin yin murabus daga muƙaminsa da ficewa daga jam'iyyar ne saboda wasu dalilai na shi na ƙashin kansa.
Wani ɓangare na wasiƙar da ya aikewa shugaban jam'iyyar na jihar na cewa:
"Na rubuto wannan wasiƙar ne domin sanar maka da hukuncin da na yanke na yin murabus daga muƙamina na sakataren jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na jiha."
"Kamar yadda karin maganar nan yake cewa komai ya yi farko zai yi ƙarshe. Saboda haka na yanke hukuncin murabus daga muƙamina ne saboda wasu dalilai na ƙashin kai na."
Gaskiyar Zance Kan Shirin Dakatar Da Bukola Saraki Daga PDP
A wani labarin kuma, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ƙwara ta bayyana cewa ba ta da shirin dakatar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.
Jam'iyyar ta yi fatali da rahotannin da ke cewa tana shirin dakatar da tsohon gwamnan na jihar daga jam'iyyar, inda tace ƙarya ce kawai tsagwaronta.
Asali: Legit.ng