Majalisar Wakilai Ta Fara Tantance Hafsoshin Tsaro Da Shugaba Tinubu Ya Tura
- Majalisar Wakilan Najeriya ta fara tantance sabbin hafsosshin tsaro da aka nada a kwanakin baya don kawo karshen rashin tsaro a kasar
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada sabbin hafsoshin tsaron ne bayan sauke wadanda ya gada a gwamnatin tsohon shugaba Buhari
- Majalisar ta na tantancewar ne a Abuja babban birnin kasar yayin da hafsoshin tsaron ke gabatar da kansu da dan takaitaccen bayani
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - 'Yan majalisar Wakilai a Najeriya yanzu haka sun fara tantance hafsoshin tsaro da shugaban kasa Bola Tinubu ya nada a kwanakin baya.
Daga cikin hafsoshin tsaron akwai Hafsan tsaro, Christopher Musa da Taoreed Lagbaja wanda shi ne shugaban sojin kasa sai Emmanuel Ogalla hafsan sojin ruwa sai kuma Hassan Abubakar a matsayin hafsan sojin sama.
A makon jiya ne Shugaba Tinubu ya tura sunayensu don tantance su a majalisar, cewar TheCable.
Tinubu ya mika sunayen hafsoshin tsaron a makon da ya gabata don tantancewa
A makon da ya gabata ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rubuta takarda zuwa majalisar Wakilai don neman tantance sabbin hafsoshin tsaron.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tinubu ya bayyana cewa wannan sauyin da aka samu a bangaren shugabannin tsaron ya zama dole don ganin an kawo karshen matsalolin tsaro a kasar.
Hafsoshin tsaron sun bayyana a gaban majalisar a yau Litinin 17 ga watan Yuli inda suke gabatar da kansu da d an takaitaccen bayani, cewar gidan talabijin Channels.
Lagbaja ya dauki alkawarin kawo karshen tsaro a gaban majalisar
Yayin da ya ke bayani a gaban ‘yan majalisar, Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya bayyana cewa zai yi aiki tare da sauran jami’an tsaro don tabbatar da sun tsare kasar daga duk wata nau’i na rashin zaman lafiya.
Ya ce ya na sane da irin matsalolin tsaro a kasar inda ya ce zai inganta sojojin kasar don kwarewa ta fannin daukar matakan gaggawa.
A cewarsa:
“Zan yi iya kokari na don tabbatar da cewa ban ba da kunya ba akan nauyin da shugaban kasa ya dauramin.”
Rashin Tsaro: Tinubu Na Ganawar Sirri Da Ribadu Da Hafsoshin Tsaro A Abuja
A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu na ganawar sirri da hafsoshin tsaron kasar da kuma mai ba da shawara a harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.
Shugaban ya nada sabbin hafsoshin tsaron ne a ranar 19 ga watan Yuni don sauya akalar tsaron kasar.
Babban Sifetan 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun shi ma ya na daga cikin mahalarta taron.
Asali: Legit.ng