Siyasar Kano: Dattijon Arewa, Yakasai Ya ba Gwamnatin Abba Gida-Gida Shawarwari

Siyasar Kano: Dattijon Arewa, Yakasai Ya ba Gwamnatin Abba Gida-Gida Shawarwari

  • Tanko Yakasai ya yi fashin baki kan yadda siyasar jihar ta ke tafiya tsakanin bangarori biyu
  • Mulki ya bar hannun Gandujiyya, ‘Yan Kwankwasiyya sun karbi Gwamnatin Kano a Mayun 2023
  • Yakasai ya ja kunnen sabuwar Gwamnati a kan tsige Sarakuna da juyawa Rabiu Kwankwaso baya

Kano - A hirar da aka yi da Tanko Yakasai kan batun siyasa da kuma sabuwar gwamnatin tarayya da ta Kano da aka rantsar a Mayun 2023.

Kamar yadda ake cewa siyasar Kano sai Kano, ‘Dan siyasar ya ce tun fil azal haka ake yi a jihar Kano, ana canza gwamnati daga jam’iyya zuwa wata.

A cewarsa, ya kamata Abba ya guji abin da zai jawo masa rigima da Rabiu Kwankwaso, kuma ya yi hattara game da tsige Sarakunan Kano.

Abba Gida Gida
Abba da Sarkin Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Yakasai ya shaidawa Sun cewa sai daga baya zai iya gane gudun ruwan Abba Kabir Yusuf, ya ce a halin yanzu gwamnan bai dade da fara mulki ba.

Kara karanta wannan

Radadin Cire Tallafi: Abba Gida Gida Ya Caccaki Tinubu Kan Wata Matsala Daya Tak, Sun Raba Gari

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ba Abba lokacin tukuna - Yakasai

"Ina ganin cewa ya kamata mu saurari Gwamna Abba, mu ba shi lokaci mu ga yadda zai shawo kan matsalolin jihar.
Mu na da ‘Yan Gandujiyya da ‘Yan Kwankwasiyya, dukkansu ba su yi bayanin yadda za a magance matslolin ba.
Zan jira in ga inda Abba zai ba fifiko da matsalolin da zai magance, in ga ko ya kama hanyar gyara, sai in auna shi."

- Tanko Yakasai

Rusau a jihar Kano

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta na ruguza gine-gine da ta ce an yi su ba a kan ka’ida ba, dattijon yana da ra’ayin akwai matsala game da lamarin.

Yakasai yake cewa idan har za a rusa gidaje da gine-ginen jama’a, ya kamata a bar doka tayi aiki, baabin da zai iya bada damar yin bita-da-kulli ba.

Kara karanta wannan

Ana Shirin Kinkimo Ƙanin Tsohon Gwamna, a ba shi Minista a Gwamnatin Tinubu

Ya dace a sauke Sarakuna?

"Ban san me Kwankwaso yake so a nan gaba ba. Amma ban jin dadin gwamnati ta karbi mulki ta fara tsige mutanen da magabatanta su ka nada ba.
Domin hakan zai jawo da zarar an canza gwamnati, a cigaba da yin irin haka. Wannan zai kawo a rika kawo tsare-tsare saboda ramuwar gayya."

- Tanko Yakasai

Rikicin siyasa a Benuwai

A wani rahoton, an ji cewa Gwamnatin Benuwai ta kafa kwamiti na musamman da zai binciko kayan da aka sace a lokacin mulkin Samuel Ortom.

Kwamitin da ke wannan aiki ya yi awon gaba da motoci daga garejin tsohon Gwamnan jihar. Sai dai jam'iyyar PDP ta soki wannan lamari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng