EFCC Ta Koma Kotu da ‘Dan Takaran APC Kan Zargin Damfarar Larabawa $1.3m

EFCC Ta Koma Kotu da ‘Dan Takaran APC Kan Zargin Damfarar Larabawa $1.3m

  • Abdulsalam Abdulkarim Zaura ya sake komawa kotu bayan Alkali ya bukaci a maimaita shari’arsa
  • Hukumar EFCC ta na zargin ‘Dan takaran na Sanatan tsakiyar Kano a 2023 ya tafka damfarar $1.3m
  • An gagara cigaba da sauraron karar domin kotun tarayya ta ce dole a ji hukuncin kotun koli tukuna

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - A zaman da aka yi karshe a makon nan, babban kotun tarayya da ke garin Kano ta daga batun sake yin shari’a da Abdulsalam Abdulkarim Zaura.

Daily Trust ta ce hukumar EFCC ta kai Abdulsalam Abdulkarim Zaura gaban kotu bisa zargin cewa ya tafka satar fam Dala miliyan $1.3 a kasar Kuwait.

A ranar Alhamis, Lauyoyin EFCC su ka sake gurfanar da ‘dan siyasar da aka fi sani da A.A Zaura da ya yi takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

APC Ta Tsure da PDP Ta Kawo Hujjoji a Kotu Domin Karbe Kujerar Gwamnan Kaduna

EFCC.
EFCC tana shari'a da Abdulsalam Abdulkarim Zaura Hoto: dailypost.ng
Asali: Twitter

Wannan karo EFCC ta zargi Zaura da aikata laifuffuka hudu, daga ciki akwai yaudarar Kuwait da sunan ya mallaki kadarori a kasashen Larabawa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A ranar 1 ga watan Maris Hukuma ta sake komawa kotu da shi a sakamakon hukuncin kotun daukaka kara da ya bukaci a sake sauraron shari’arsu.

Ishaq Mudi Dikko ya gabatar da hujja

Jaridar ta ce Lauyan da yake kare jigon na jam’iyyar APC a jihar Kano, Ishaq Mudi Dikko (SAN), ya shaidawa kotu cewa sun kai kara zuwa gaban kotun koli.

Dikko yake cewa sun bukaci Alkalan kotun koli su hana kotu ta kuma dauko shari’ar.

Ko da Lauyan wanda ake kara ya bukaci ayi wa kotu biyayya, Lauyan EFCC ya nuna ba su yarda ba, ya ce dokar ACJA ta hana yin haka saboda an daukaka kara.

Kara karanta wannan

Shehu Sani Ya Yi Hasashen Abun da Zai Faru Idan Kotu Ta Tsige Shugaban Kasa Tinubu

Hukuncin Muhammad Yunusa

Mai shari’a Muhammad Yunusa ya yanke hukunci cewa kotun koli ce gaba da kowace kotu, saboda haka ya fi karkata da rokon Lauya mai bada kariya.

Alkalin kotun ya ce azarbabi ne yin hukunci a kan lamarin alhali ba a gama sauraron daukaka karar da bangaren wanda ake tuhuma su ka yi a kotun koli ba.

A karshe, kotu ta dakatar da sauraron shari’ar har sai ranar da kotun koli tayi hukunci.

Siyasar Ebonyi ta zama 'yar gida daya

A rahoton da mu ka samu, shugaban SNM, Solomon Semaka ya ce Sanata Dave Umahi ya kai sunan ‘danuwansa na jini domin Bola Tinubu ya ba shi Minista.

Idan gaskiya ne, tsohon Gwamnan yana so jigon na APC, Mista Austine Umahi ya samu kujerar Ministan tarayya yayin da shi kuma yake majalisar dattawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng