Kotu Ta Yi Fatali Da Karar Da Aka Shigar Kan Nasarar Gwamna Makinde Na Jihar Oyo
- Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya yi nasara a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar
- Kotun ta yi fatali da ƙarar da jam'iyyar APM ta shigar inda ta ke ƙalubalantar nasarar da gwamna Makinde ya yi a zaben gwamna
- Kotun ta kuma ci tarar jam'iyyar APM saboda wasa da hankalin kotu da ɓata lokacin waɗanda ake ƙara
Jihar Oyo - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Oyo, ta yi fatali da ƙarar da jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM) ta shigar inda ta ke ƙabulantar nasarar gwamna Seyi Makinde.
Jam'iyyar APM na ƙalubalantar hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) kan sanar da Makinde na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri'u 563,756.
Jaridar The Punch tace a hukuncin da kotun ta yanke, wanda shugabar kotun mai shari'a Ejiron Emudainohwo ta karanto, ta yi fatali da ƙarar inda ta umarci jam'iyyar APM ta biya tarar N1m ga gwamna Makinde da jam'iyyar PDP.
Kotun ta bayyana dalilin cin tarar jam'iyyar APM
Emudainohwo ta bayyana ƙarar a matsayin wasa da hankalin kotu, inda ta ƙara da cewa akwai lauje cikin naɗi shigar da ƙarar da aka yi kwanaki 46 bayan jam'iyyar tana sane da cewa ɗan takararta baya son ƙarar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta bayyana cewa dole ne jam'iyyar ta biya kuɗin saboda ɓata wa waɗanda ake ƙara lokaci wajen tattaro bayansu da ɓata wa kotun lokaci, cewar rahoton The Nation.
Emudainohwo tace tilasta biyan kuɗin zai zama gargaɗi ga jam'iyyar domin ta shiga taitayinta nan gaba.
Tun da farko, lauyan jam'iyyar APM, Mr Henry Bello, ya gayawa kotun cewa ya nemi da a janye ƙarar da jam'iyyar ta shigar akan Makinde.
Bello ya bayyana cewa ɗan takarar jam'iyyar, Mr Adeniran Oluwaseyi wanda aka shigar da ƙarar dominsa ya sare dangane da ƙarar, inda har ya taya gwamna Makinde murnar nasarar da ya samu.
Shugaban APC Na Kasa Adamu Ya Ce Ba Tinubu Ba Ne Dan Takararsa a Zaben Fidda Gwani, Ya Bayyana Wanda Ya Marawa Baya
Butulci Aka Yi Mana a Oyo, Dan Takarar Gwamnan APC
A wani labarin kuma ɗan takarar gwamnan jam'iyyar APC a jihar Oyo, Teslim Folarin ya koka kan yadda aka yi masa butulci a zaɓen gwamnan jihar.
Folarin ya bayyana cewa an shirya wata ƙulla-ƙulla ne a zaɓen saboda nasarar Shugaba Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng