Abba Gida-Gida: Za a Tura Naƙasassun jihar Kano Zuwa Jami’o’in Kasashen Waje
- Gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta aika masu nakasa zuwa kasashen waje domin yin digirgir
- Kwamishinan ilmi na Kano, Umar Haruna Doguwa ya tabbatar da wannan ya zanta da ‘yan jarida
- Aika yara zuwa makarantu domin karo ilmi yana cikin tsare-tsare da manufofin Kwankwasiyya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kano - Gwamnatin jihar Kano za ta bada damar zuwa karo karatu a kasashen ketare ga hazikan mutane masu basira da ke fama da nakasa.
Kwamishinan harkar ilmi, Umar Haruna Doguwa ya shaida cewa tsarinsu na bunkasa ilmi zai shafi nakasassu, Punch ta kawo labarin.
Idan har wadannan Bayin Allah su na da takardun da ake bukata domin karo ilmi a waje, Umar Haruna Doguwa ya ce su amfana da tsarin.
Jawabin Kwamishinan ilmi
"Yana cikin tsarin gwamnatin nan na tabbatar da adalci wajen samun ilmi ga kowane ‘dan jihar, kamar yadda yake a dokokin kasashen waje.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Shakka babu za mu bada damar zuwa karatu ga masu matakin digiri na farko da na biyu, har da masu nakasa
Za a taimaka masu domin su yi rayuwa mai kyau, sannan kuma su amfani da al’umma."
- Umar Haruna Doguwa
Rahoton ya ce Doguwa ya yi wannan karin haski ne da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida bayan wasu kungiyoyi sun kai masa ziyara a ofishinsa.
Ba a nan kurum, gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta tsaya ba, Kwamishinan ya ce za su duba yiwuwar kafa makarantu na musamman a fadin Kano.
A hada kararun digirgir da tallafin digiri
Aisar Fagge, malamin makaranta ne kuma ‘dan jarida, ya shaidawa Legit.ng Hausa cewa yana goyon bayan a tura matasa zuwa jami’o’in waje.
A daidai wannan lokaci kuma Fagge ya ce yana da kyau a tallafawa daliban gida da aka karawa kudin makaranta a jami’o’in gwamnatin kasar.
"Ya kamata Gwamnati tayi tsari, kyau ta duba aljihunta, ta bada tallafin 50% ko 100% na kudin makaranta, haka zalika Sanatoci da ‘yan majalisu.
Kullum talakawa na kukan cewa ba za su iya biyan wadannan kudi ba, idan kuwa babu kudin karatu, a karshe dole su hakura da karatun gaba daya."
- Aisar Fagge
Kurame za su yi farin ciki
Malam Yasir Sulaiman Kofa wanda yake yi wa kurame tafinta a Kaduna, ya yaba da lamarin, ya ce tsari ne mai kyau domin su ma su na neman ilmi.
A cewarsa, masu nakasa su ne asalin wadanda ke bukatar tallafin karatu a irin halin da ake ciki.
Babu nadama a kan rushe-rushe
A yau aka ji Gwamnatin jihar Kano ta ce ba ta yi nadama ba kan rushe-rushen da take gudanarwa a 'yan kwanakin nan ba, duk da surutun jama'a.
Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan, yake cewa ɗaya daga cikin alƙawuran da suka yi kenan.
Asali: Legit.ng