Yadda APC Ta Hana Tinubu Kudi a Lokacin Kamfe In Ji Mataimakin Shugaban Jam’iyya

Yadda APC Ta Hana Tinubu Kudi a Lokacin Kamfe In Ji Mataimakin Shugaban Jam’iyya

  • Mataimakin shugaban APC na Arewa maso yamma, ya maida martani a kan sukarsa da aka yi
  • Salihu Lukman ya samu lokaci ya yi kaca-kaca da Iyiola Omisore, ya hada da Abdullahi Adamu
  • Lukman ya kira taron ‘yan jarida, ya fada masu abin da ya faru da Bola Tinubu lokacin yin kamfe

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Salihu Lukman wanda shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso yamma, ya dauki zafi a rikicin da ake yi da shi.

A ranar Laraba, Vanguard ta ce Alhaji Salihu Lukman ya zargi Abdullahi Adamu da Iyiola Omisore da yi wa APC riko tamkar wasu azzaluman Sarakai.

Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, shugaba a jam’iyyar mai ci ya ce shugaban APC na kasa da sakatarensa sun sauka daga tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Fara da Kyau Amma Tun Farko na San Babu Inda Buhari Zai Je - Dattijon Arewa

Shugabannin APC
Shugaban Jam’iyyar APC Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Raddi ga Sanata Iyiola Omisore

Wannan martani ne da Lukman ya maidawa bayan Sanata Iyiola Omisore ya kamanta zaman shi a jam’iyyar APC da bakar tinkiya cikin dabbobi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Game da Abdullahi Adamu da ya ce bai san da zaman shi ba, mataimakin na sa ya ce wannan matsalarsa ce, amma shi ya dade sosai a cikin tafiyar APC.

A cewarsa, babu wani shugaba a jam’iyyarsu ta APC da zai ce bai san da gudumuwar shi ba tun daga lokacin Adams Oshiomhole zuwa Mai Mala Buni.

A karkashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu, tsohon Darekta Janar din na PGF ya ce an toshe kofar muhawara a APC ta kai babu cigaba a jam’iyyar.

Batun kudi da yakin zabe

Alhaji Lukman ya ce shugabannin jam’iyyar sun samu N30bn, amma abin da aka rabawa 'yan jam'iyya a jihohi 36, bai wuce Naira miliyan 700 rak ba.

Kara karanta wannan

Tinubu Na Shirin Bin Tsarin Da Buhari Ya Bi Wajen Bayyana Ministocinsa, Bayanai Sun Fito

Wani zargi mai nauyi da ‘dan siyasar ya jefi shugabanninsa da shi kuwa shi ne rashin taimakawa Bola Tinubu da kudi a kakar yakin neman zabe.

Rahoton The Cable ya nuna Lukman ya ce uwar jam’iyya ba ta taimakawa Tinubu da sisin kobo a lokacin da ya ke neman zama shugaban Najeriya ba.

Shi (Bola Tinubu) bai samu ficika daga hannun jam’iyya ba. Na fito fili ina fadan wannan. Su fito su kalubalance ni, su ja da ni.”

- Salihu Lukman

Shari'ar zaben shugaban kasa

A wannan rahoto, shugaban jam’iyyar LP na kasa, Barista Julius Abureya ce wadanda su ke gwamnati sun fara shiryawa mai-man zaben 2023.

Abure ya ce dole mu ma mu fara shiryawa domin gudun wadanda su ke cikin gwamnati su mamaye mu, a cewarsa Peter Obi ne ya lashe zaben bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng