Gwamna Zulum Ya Nada Tijani Bukar a Matsayin Sabon Sakataren Gwamnatin Jihar
- Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya naɗa sabon sakataren gwamnatin jihar (SSG)
- Gwamnan ya amince da naɗin Bukar Tijani a matsayin sabon SSG a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Isa Gusau ya fitar a ranar Laraba
- Tijani ya taɓa riƙe muƙamin minista a gwamnatin tsohon shugaba Goodluck Jonathan kafin daga nan ya wuce majalisar ɗinkin duniya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Borno, Maiduguri - Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya naɗa Bukar Tijani, tsohon ministan shugaba Goodluck Jonathan, a matsayin sakataren gwamnatin jihar.
Jaridar Punch ta rahoto cewa mai magana da yawun gwamnan, Isa Gusau, shine ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 12 ga watan Yuli.
Tijani, wanda tsohon ƙaramin ministan noma ne da raya karkara, ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin Sakataren majalisar ɗinkin duniya/mataimakin babban darektan hukumar noma da abinci.
"Ku Cire Tsoro" Gwamnan Arewa Ya Yi Karin Haske Kan Matakai 2 da Zai Ɗauka Kan Malamai 7,000 A Jiharsa
Sanarwar ta tabbatar da cewa gwamna Zulum ya naɗa Tijani matsayin sakataren gwamnatin jihar ne bayan ya gamsu da ƙwarewar da yake da ita.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tarihin Tijani
A cewar rahoton Vanguard, an haifi Tijani mai shekara 62 a duniya a ƙauyen Damasak cikin ƙaramar hukumar Dikwa ta jihar Borno.
Ya yi karatun Firamarensa a makarantar Firamaren Monguno daga shekarar 1967 zuwa 1970 da makarantar Firamare ta Gubio daga shekarar 1970 zuwa 1973. Sannan ya yi karatun Sakandire a makarantar Sakandiren gwamnati ta Maiduguri daga shekarar 1973 zuwa 1978.
Ya yi digirinsa na farko a fannin kimiyyar tsirrai da ƙasa daga shekarar 1982 zuwa 1994 a kwalejin Tuskegee (wacce yanzu ta koma jami'ar Tuskegee) a birnin Alabama na ƙasar Amurka.
Tijani ya yi digirin digirgir a jami'ar Reading da ke UK a shekarar 1989.
Gwamna Zulum Ya Samar Da Motocin Kai Manoma Gonakinsu
A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya samar da motocin da za su riƙa jigilar manoma zuwa gonakinsu a jihar Borno.
Gwamnan ya sanar da samar da motoci 300 waɗanda za su yi jigilar manoman domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Tinubu ta yi a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng