APC Ta Tsure da PDP Ta Kawo Hujjoji a Kotu Domin Karbe Kujerar Gwamnan Kaduna

APC Ta Tsure da PDP Ta Kawo Hujjoji a Kotu Domin Karbe Kujerar Gwamnan Kaduna

  • Lauyoyin Uba Sani sun kalubalanci amfani da asalin takardun INEC a matsayin hujjoji a kotu
  • ‘Dan takaran Gwamna Kaduna a PDP, Mohammed Isah Ashiru bai gamsu da sakamakon zaben ba
  • Duro Adeyele SAN yana ganin bai dace a kinkimo ainihin takardun aikin zabe, a kai wa Alkalai ba

Kaduna - Gwamna Uba Sani bai yarda da hujjojin da ake kokarin ayi amfani da su daga hukumar INEC a gaban kotun sauraron karar zaben shi ba.

Baya ga kin amincewa ayi amfani da wadannan takardu, Daily Trust ta ce Mai girma Uba Sani ya na so kotu tayi watsi da karar da jam’iyyar PDP ta kai.

Lauyan da yake kare Uba Sani wanda shi ne ‘dan takaran APC a zaben bana, ya soki karar PDP.

Kara karanta wannan

Jami’an Gwamnati Sun Dura Gareji, An Yi Awon Gaba da Motocin Tsohon Gwamna

Gwamna Uba Sani
Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Duro Adeyele zai kawo hujjoji

Duk abin da aka yi, Lauyan Gwamnan watau Duro Adeyele (SAN) bai fadawa kotu dalilinsa na neman kin karbar hujjojin da Lauyan PDP ya kawo ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Cif Adeyele (SAN) ya ce za su gabatar da korafinsu a rubuce, su gabatarwa kotun korafin zaben.

Jam’iyyar PDP da ‘dan takaranta, Hon. Mohammed Isah Ashiru su na kalubalantar APC da Hukumar INEC kan zaben Gwamnan Kaduna da aka shirya.

Sakamakon zaben Kananan hukumomi 14

This Day ta ce kamar yadda kotu tka bukata, hukumar INEC ta gabatar da takardun EC8A, EC8B, da EC8C daga kananan hukumomi tara na jihar Kaduna.

Kananun hukumomin sun kunshi Kubau, Lere, Kudan, Birnin Gwari, Igabi, Zaria, S/Gari, da kananan hukumomin Kaduna ta Arewa da Kaduna ta Kudu.

Lauyan INEC, A.M. Aliyu (SAN) da na APC su na da ra’ayin cewa bai dace a dauko asalin takardun da INEC ta mallaka, a kawo su gaban kotun zabe ba.

Kara karanta wannan

Shehu Sani Ya Yi Hasashen Abun da Zai Faru Idan Kotu Ta Tsige Shugaban Kasa Tinubu

Da ake sauraron karar, lauyoyin da ke bada kariya sun ce kamata ya yi PDP ta nemi takardun daga INEC. A yau ne za a cigaba da sauraron wannan kara.

Wani lauyan PDP da ya zanta da ‘yan jarida a ranar Talata, Giovanni Laah, ya shaida cewa su na bukatar ainihin hujjojin ne kafin su fara kiran shaidunsu.

Rikici a Jam'iyyar APC

Ana tuhumar Abdullahi Adamu da cewa bai goyi bayan Bola Tinubu ya samu takara a jam’iyyar APC ba, a kan haka aka ji labari wasu su na so a tsige shi.

A jam’iyya mai-mulki, akwai zargin da ake yi wa tsohon Gwamnan na Nasarawa na sama da fadi da wasu kudi bayan ya zama shugaban majalisar NWC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng