Shugaba Tinubu Zai Nada Ministoci 36 Zuwa 42 a Gwamnatinsa, Omisore

Shugaba Tinubu Zai Nada Ministoci 36 Zuwa 42 a Gwamnatinsa, Omisore

  • Daga ƙarshe, an bayyana yawan Ministocin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai naɗa a sabuwar gwamnatinsa
  • Sakataren APC na ƙasa, Sanata Iyiola Omisore ya ce shugaban kasa na da ikon naɗa Ministoci a tsakanin 36 zuwa 42
  • Ya ce wuƙa da nama na hannun shugaba Tinubu, idan ya so zai iya naɗa mambobin jam'iyyun adawa kamar irinsu Wike

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Sakataren jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Iyiola Omisore, ya ce shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai naɗa ministoci 36 zuwa 42 a gwamnatinsa.

Daily Trust ta tattaro cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya tilasta wa shugaban ƙasa ya naɗa minista ɗaya daga kowace jiha a Najeriya da kuma ƙarin minista ɗaya daga kowace shiyya.

Shugaban ƙasa Tinubu tare da sakataren APC.
Shugaba Tinubu Zai Nada Ministoci 36 Zuwa 42 a Gwamnatinsa, Omisore Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Idan zaku iya tuna wa, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa ministoci 36 a zangon mulkinsa na farko, amma a zango na biyu ya ƙara suka kai 42.

Kara karanta wannan

Shugaban APC Na Kasa Adamu Ya Ce Ba Tinubu Ba Ne Dan Takararsa a Zaben Fidda Gwani, Ya Bayyana Wanda Ya Marawa Baya

Adadin ministoci nawa shugaba Tinubu zai naɗa a halin yanzu?

Da yake jawabi a cikin shirin siyasa a yau na kafar watsa labaran Channels tv, Sanata Omisore ya ce yawan Ministocin da Tinubu zai naɗa na tsakanin 36 zuwa 42.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Kundin tsarin mulki ya ce minista ɗaya daga kowace jiha jimulla 36 kenan da kuma minista ɗaya daga kowace shiyya, idan muka haɗa ya zama 42, wuƙa da nama na hannun shugaban ƙasa."

"Saboda haka ko dai ya naɗa ministoci mafi ƙaranci 36 ko kuma mafi yawa 42," inji Sakataren APC na ƙasa, Omisore.

"Har yanzun muna kan aikin neman shawarin jam'iyya, muna kokarin tsara jerin ministocin. Muna fatan haɗa tawagar ministocin da zata yi daidai da bukatar 'yan Najeriya."

Shin Tinubu zai naɗa waɗan da ba mambobin APC ba?

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Shirya Karban Gwamnonin PDP 5 Da Zaran Sun Shirya Sauya Sheƙa Zuwa Cikinta

Yayin da aka tambaye shi ko shugaba Tinubu na tunanin kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa tare da mambobin jam'iyun adawa kamar Nyesom Wike, Omisore ya ce wuƙa da nama na hannun shugaban ƙasa.

Ya ce a halin yanzun shugaban kasa na ci gaba da tattaunawa da jam'iyya mai mulki dangane da sunayen ministocin da zai naɗa, kamar yadda Dailypost ta ruwaito.

Shugaba Bola Tinubu Na Daf Da Bayyana Sunan Sabon Wanda Ya Nada Mukami

A wani labarin na daban kuma mun kawo muku rahoton cewa Shugaba Bola Tinubu yana shirin sanar da sabon wanda ya nada mukami kowanne lokaci daga yanzu.

Ana sa ran nan ba da dadewa ba Shugaban Kasar zai sanar da Hakeem Muri-Okunola, shugaban ma'aikatan jihar Legas , a matsayin babban kebabban sakatarensa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262