Jerin Ministoci: Sunayen Tsaffin Gwamnoni Da Suka Taba Yin Minista Da Za Su Iya Dawowa

Jerin Ministoci: Sunayen Tsaffin Gwamnoni Da Suka Taba Yin Minista Da Za Su Iya Dawowa

Shugaba Tinubu yana da ragowar kwana 20 domin sanar da ministocinsa nan da ranar 28 ga watan Yuli, lokacin da zai cika kwana 60 akan karagar mulki.

Biyo bayan sabuwar dokar da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu, shugaban ƙasa da gwamnoni za su bayyana sunayen ministoci da kwamishinoni ne a cikin kwana 60 da hawa mulki.

Tsaffin yan siyasa da za su iya samun minista a karkashin Tinubu
Wasu daga cikin tsaffin yan siyasar za su iya sake zama ministoci Hoto: Nyesom Wike
Asali: Twitter

Lokacin da Shugaba Tinubu zai bayyana ministocinsa

A yayin da shugaba Tinubu yake shirin bayyana ministocinsa, akwai alamu da su ke nuna cewa akwai wasu ƴan siyasa da suka taɓa riƙe muƙaman gwamna da minista waɗanda za a iya gani a cikin ministocin.

Ga wasu daga cikinsu da ake ganin za su iya shiga cikin jerin ministocin Tinubu:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yanzu: Shugaba Bola Tinubu Na Shirin Nada Tsohon Hadiminsa Mukami Mai Muhimmanci

Babatunde Fashola

Fashola ya kasance aminin Bola Tinubu tun lokacin da yake gwamnan jihar Legas. Fashola ya yi minista har sau biyu a gwamnatin tsohon shugaba Muhammadu Buhari.

Tsohon ministan ya gaji Tinubu a matsayin gwamnan Legas, sannan zai iya zama minista a wannan gwamnatin ta yanzu.

Nasir El-Rufai

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya taɓa yin ministan babban birnin tarayya Abuja a ƙarƙashin gwamnatin Olusegun Obasanjo daga shekarar 2003 zuwa 2007.

Akwai yiwuwar El-Rufai ya sake zama minista a gwamnatin Tinubu, duba da irin gudunmawar da ya bayar wajen nasarar jam'iyyar APC da Shugaba Tinubu a babban zaɓen 2023.

Nyesom Wike

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya taɓa riƙe muƙamin ƙaramin ministan ilmi a watan Yulin 2011 inda daga bisani aka mayar da shi ministan ilmi a ƙarƙashin gwamnatin tsohon shugaba Goodluck Jonathan.

Wike ya sauka daga kan wannan muƙamin domin takarar gwamnan jihar Rivers a shekarar 2015. Ya samu nasara a zaɓen inda ya riƙe kujerar gwamna har sau biyu.

Kara karanta wannan

Yadda Sabon Tsarin Shugaba Tinubu Ya Tilasta Gwamnonin PDP Biyu Rage Yawan Ma'aikatu a Jihohinsu

Tsohon gwamnan zai iya zama minista a APC duk da ya kassnce ɗan jam'iyyar PDP ne.

Kayode Fayemi

Fayemi ya riƙe muƙamin minista a gwamnatin tsohon shugaba Buhari daga watan Nuwamban 2015 har zuwa watan Mayun 2018, lokacin da ya yi murabus domin yin takarar gwamnan jihar Ekiti wanda ya lashe.

Tsohon gwamnan ya janye takararsa saboda Tinubu a lokacin zaɓen fidda gwanin shugaban ƙasa na APC, bayan shugabannin APC na yankin Kudu maso Yamma sun nemi dukkanin ƴan takarar da suka fito daga yankin su janyewa Tinubu.

Za a iya saka masa da muƙamin minista a dalilin hakan.

Rabiu Kwankwaso

Tsohon gwamnan na jihar Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP, yana cikin masu neman minista daga jihar tare da tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Kwankwaso ya taɓa yin ministan tsaro a ƙarƙashin gwamnatin Olusegun Obasanjo.

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya gana da Shugaba Tinubu a ƙasar Faransa, wanda hakan har ƙura ya tayar a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

"Ku Cire Tsoro" Gwamnan Arewa Ya Yi Karin Haske Kan Matakai 2 da Zai Ɗauka Kan Malamai 7,000 A Jiharsa

Tsohuwar 'Yar Takara Na Son Mukamin Minista

A wani labarin na daban kuma, tsohuwar ƴar takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC, ta buƙaci Shugaba Tinubu ya bata muƙamin minista.

Joy Ibinabo Dokubo ta bayyana cewa ta cancanci zama minista saboda gudunmawar da ta ba jam'iyyar APC da Shugaba Tinubu a lokacin zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng