‘Dan Majalisa Ya Ja-Kunnen Tinubu, Ya Nuna Masa Ya Yi Hattara da Wani Gwamnan APC

‘Dan Majalisa Ya Ja-Kunnen Tinubu, Ya Nuna Masa Ya Yi Hattara da Wani Gwamnan APC

  • Ikenga Imo Ugochinyere Ikeagwuonu ya fitar da jawabi da ya yi kaca-kaca da Sanata Hope Uzodimma
  • ‘Dan majalisar ya zargi Gwamnan Imo da hada-kai da shugaban APC domin a kawowa Bola Tinubu cikas
  • Hon. Ikeagwuonu ya ce tun zaben tsaida gwani, Gwamna Uzodimma bai goyi bayan takarar Tinubu ba

Abuja - ‘Dan majalisa mai wakiltar Arewaci da Kudancin Ideato, Ikenga Imo Ugochinyere Ikeagwuonu, ya soki gwamnan Imo, Hope Uzodimma.

Hon. Ikenga Ugochinyere Ikeagwuonu ya kira Mai girma Hope Uzodimma da masharrancin Gwamna, Leadership ta fitar da rahoton a ranar Talata.

Ikenga Ugochinyere Ikeagwuonu ya nuna Uzodimma tamkar ungulu ne da kan zabo, yake cewa jam’iyyar APC tayi kuskuren nada shi shugaban Gwamnoni.

Uzodimma da Bola Tinubu
Gwamna Hope Uzodimma da Bola Tinubu Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Bai goyon bayan Tinubu

A jawabin da ya fitar, Hon. Ugochinyere ya zargi Gwamnan Imo da kuma Abdullahi Adamu da yakar Bola Tinubu a zaben tsaida ‘dan takaran shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Dawo Najeriya, Gbajabiamila da Ganduje Sun Tarbo Shi a Filin Jirgi

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamar yadda rahoton ya bayyana, ‘dan majalisar tarayyar ya kai ga tuhumar wadannan mutum biyu da kokarin kawowa gwamnatin Bola Tinubu cikas.

“Har gobe Uzodinma yana jin haushin kunyar da ya sha kafin zaben tsaida gwanin APC, ya gagara hana Tinubu samun tikiti...
a kan tsohon abokinsa, Ahmed Lawan. Uzodinma ya ci burin zai zama ‘dan takaran mataimakin shugaban kasa tare da Lawan.

- Ikenga Imo Ugochinyere Ikeagwuonu

Babu rigima a majalisar tarayya

Abin da jigon na APC yake kokarin nunawa shi ne ‘yan majalisa su na goyon bayan shugabannin da aka zaba, akasin abin wasu su ke neman riyawa.

Don haka ‘dan siyasar ya fadawa shugaba Tinubu ya yi hattara da Uzodimma, kuma ya na rokon DSS ta taka masa burki tun kafin lamarinsa ya yi nisa.

Duk kashe-kashen da ake yi, ‘dan majalisar na Ideato ya ce babu laifin kowa illa Gwamna, ya kara da cewa ran mutum ya zama banza a mulkinsa.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Yi Jawabi da Jin Tinubu Ya Zama Sabon Shugaban Kungiyar ECOWAS

Rikicin shugabanci a majalisa

Kwanaki aka ji labari Gwamnan ya dauki abokan aikinsa zuwa wajen shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu a game da sabanin da aka samu kan majalisa.

Sanata Adamu ya nesanta kan shi daga aikin Godswill Akpabio da Tajudeen Abbas, ‘dan majalisar yana ganin ba kowa ya jawo sabanin ba sai Gwamnan Imo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng