El-Rufai Ya Bayyana Yadda Dattawan Kiristoci Kudancin Kaduna Suka 'Muzanta' Mataimakansa Daga Yankinsu
- Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya koka kan yadda dattawan Kiristocin Kaduna ta Kudu suke muzanta mataimakansa daga yankin
- Ya ce a dalilin kin jinin da suke wa Barnabas Bala, sun yi ta kokarin tuge shi a kujerarsa tun farkon shekaru biyu na mulki
- Ya kuma bayyana yadda ya yanke shawarar daukar mace Musulma daga yankin, amma duk da haka gabar ta ci gaba
Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana yadda dattawan Kaduna ta Kudu suka ci mutuncin mataimakansa daga yankin.
El-Rufai ya bayyana haka ne yayin wata lakca a ranar Asabar 8 ga watan Yuli a jami'ar Lagos.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kuma bayyana yadda ya yanke shawarar zaban Musulma daga Kaduna ta Kudu a matsayin mataimakiyarsa, cewar Premium Times.
Yadda dattawan Kaduna ta Kudu suka matsawa mataimakan El-Rufai
Jihar Kaduna ta kasu kashi uku, Kaduna ta Tsakiya da Arewa wanda mafi yawanci Musulmai ne sai kuma Kaduna ta Kudu da suke Kiristoci.
A bisa al'ada, gwamnoni Musulmai na daukar mataimakansu Kiristoci daga Kaduna ta Kudu.
El-Rufai ya ce a farkon wa'adinsa ya zabi Barnabas Bala amma dattawan nan sai da suka cire shi da karfi cikin a wa'adin na farko.
Ta ce dattawan Kiristocin na jin haushi saboda bai nada wanda suka zaba masa ba, cewar TheCable.
Har ila yau, El-Rufai ya ce dattawan sun ki jinin Mista Bala saboda kabilar da ya fito ta Moroa ba ta da tasiri tun da ba daga Kagoro ko Atyap ko Bajju ko Jaba ya fito ba.
Ya ce:
"An bukaci Bantex ya ajiye aiki har sau uku cikin shekaru biyu na mulki, da kyar Bantex ya karasa wa'adin farko.
"Saboda kiyayya daga yankin, Bantex ya rasa tikitin sanata na yankin a 2019, bayan shekara daya kuma ya ce ga garinku."
Ya yanke shawarar daukar mace Musulma mataimakiya
A dalilin haka El-Rufai ya ce ya yanke shawarar daukar mace Musulma daga yankin, amma duk da haka gabar ba ta gushe ba, Ground News.
Ya kara da cewa:
"Zaban Hadiza Bala a matsayin mataimakiya shima ya samu tasgaro irin na Bantex, sai dai duk wanda ci gaban kasa ne a gaban shi ba zai damu da wannan ba."
Nasir El-Rufai Ya Magantu Kan Kamun Ludayin Gwamnatin Tinubu
A wani labarin, tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yabi salon mulkin shugaban kasa, Bola Tinubu.
El-Rufai ya ce irin matakan da shugaban ke dauka ya nuna muhimmancin nada mukamai bisa kwarewa.
Ya ce irin matakan da shugaban ya dauka a kankanin lokaci ya sauya akalar kasar zuwa hanya mai kyau.
Asali: Legit.ng