Kwana 42 Bayan Kama Aiki, Gwamnatin Bola Tinubu Ta Gaza Cika Wani Alkawari Daya Da Ta Dauka Wa Yan Najeriya
- Tun kafin rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa, kakakinsa, Dele Alake ya ce za su fitar da sunayen ministoci a cikin wata daya
- Tinubu wanda aka rantsar a ranar 29 ga watan Mayu, dole ya tura sunayen ministoci zuwa majalisa don tantancewa kafin 29 ga watan Yuli
- A yanzu ‘yan Najeriya sun zaku su ga an fitar da sunayen ministoci daga jihohi daban-daban don ci gaba da gudanar da mulki yadda ya dace
FCT, Abuja – Bayan kwanaki 42 da darewa karagar mulki, gwamnatin Bola Tinubu ta gagara cika alkawari daya babba da ta dauka.
Yanayin yadda ‘yan Najeriya suka matsu su ga ko su san su waye suka cika jerin sunayen ministocin shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi yawa.
Minista a ko wace gwamnati na da matukar tasiri a tsare-tsaren shugaban kasa da kuma sauya akalar wasu al’amura a kasar.
Tinubu ya gaza cika alkawarin da ya dauka wa 'yan najeriya
Idan ba ku mantaba, kakakin shugaban, Dele Alake ya yi wa ‘yan Najeriya alkawarin sake sunayen a cikin wata daya sabanin tsohon shugaba Buhari da sai da ya yi watanni shida babu ministoci.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar Alake kamar yadda Punch ta tattaro a ranar 19 ga watan Maris:
“Wata daya ya yi yawa ga duk wata gwamnati mai yi da gaske ta fitar da sunayen ministocinta don gudanar da mulki yadda ya dace bayan rantsarwa.”
Yayin da a ranar 6 ga watan Yuli, Alake ya sauya magana inda ya ke cewa dalilin rashin fitar da sunayen shi ne don ganin an zakulo kwararru a gwamnatin.
Bayanin Dele Alake akan cire sunayen ministocin
Leadership ta tattaro Alake ya na cewa:
“Kun san wannan shi ne shugaban kasa, ba wai muna gunadar da tsarin mulki na majalisa ba ne.
“Don haka, komai na kan teburinsa, shi ya ke yanke hukuncin waye ya dace da shiga cikin ministocin.”
Legit.ng ta tattaro cewa, shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya rage masa saura kasa da kwanaki 18 a cikin 60 da kundin tsarin mulki ya ba shi daman tura sunayen ministoci zuwa majalisar dattawa don tantancewa.
Gwamnan PDP Mai Karfin Fada A Ji Ya Samu Shiga Jerin Ministocin Tinubu
A wani labarin, ta tabbata tsohon gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi ya samu shiga jerin sunayen ministoci.
Tun bayan rantsar da Shugaba Bola Tinubu 'yan Najeriya ke ta jiran ganin wadanda za su fito a jerin sunayen.
Saura kwanaki 18 wa'adin tura ministocin zuwa majalisar dattawa ta cika kamar yadda doka ta tanadar.
Asali: Legit.ng