Mukhtar Shehu Shagari Ya Fita Daga PDP Bayan Shekaru 24, Ya Bada Dalili

Mukhtar Shehu Shagari Ya Fita Daga PDP Bayan Shekaru 24, Ya Bada Dalili

  • Babban jam'iyyar hamayya ta Peoples Democratic Party (PDP) ta rasa daya cikin manyan jiga-jiganta
  • Alhaji Mukhtar Shagari ya fice daga PDP ya shiga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki bayan shafe shekaru 24
  • Tsohon Ministan Ayyukan Noma da Albarkartun Ruwan ya ki bayyana dalilinsa na komawa APC

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Tsohon ministan noma da albarkatun ruwa, Alhaji Mukhtar Shehu Shagari ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Tsohon mataimakin gwamnan na jihar Sokoto, Shagari ya yi murabus daga jam'iyyar PDP kuma ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Mukhtar Shehu Shagari ya fita daga PDP
Tsohon ministan ayyukan noma da albarkarun ruwa, Mukhtar Shehu Shagari ya fita daga PDP ya koma APC. Hoto: Mukhtar Shehu Shagari
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mukhtar Shehu Shagari ya fice daga PDP bayan shekaru 24

Ya sanar da hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Asabar, 8 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Ana Tsaka da Dakon Sunayen Minustoci, Ɗan Takarar Gwamna Ya Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa AapC

Muktar Shehu Shagari @MukhtarShagari, ya ayyana a ranar Asabar 8 ga watan Yuli cewa, "Yanzu na koma APC, Insha Allah."

A amsar da ya bai wa Nigerian Tribune cikin sakon kar ta kwana, a ranar Lahadi, 9 ga watan Yuli, na neman ya yi karin haske kan dalilinsa na komawa APC, tsohon minista Shagari ya amsa da cewa:

"Da gaske ne na koma jam'iyyar APC, amma ba ni da niyyar yin wata magana kan hakan a yanzu."
Mukhtar Shehu Shagari ya bada dalilin komawa jam'iyyar APC
Da ya ke magana kan dalilinsa na komawa APC, @MukhtarShagari, ya ce:
"Ba wai don abin da za a samu bane, saboda mutunci ne."

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164