Tsohon Gwamnan Ekiti Ya Ambaci Jigon PDP da Wajibi Yana Cikin Ministocin Tinubu
- Ayodele Peter Fayose ya na ganin bai dace Bola Tinubu ya kafa gwamnati ba tare da Nyesom Wike ba
- Tsohon Gwamnan kuma jagoran PDP ya ce ‘Yan G5 ba su sauya-sheka daga jam’iyyarsu ta PDP ba
- Idan za ayi rabon mukamai, a ra’ayin Fayose wajibi ne Wike ya samu wuri a gwamnatin Tinubu
Abuja - Tsohon Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Peter Fayose ya shaida cewa ya zama dole a mutunta kokarin da G5 tayi wa Bola Ahmed Tinubu a 2023.
Da aka tattauna da shi a gidan talabijin Channels, Ayo Peter Fayose ya nuna ‘yan kungiyar G5 ko Integrity Group sun ba APC gudumuwa wajen takara.
A nan aka ji ‘dan siyasar ya na cewa Nyesom Wike ya na da duk abin da ake nema na cancanta wajen zama Minista a karkashin gwamnatin Bola Tinubu.
Dole a tafi da Shugaban G5
Fayose ya na ganin cewa ya zama dole shugaban ‘yan tafiyar G5 din ya samu kujera a gwamnati mai-ci saboda irin rawar da ya taka waje kifar da PDP.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Duk da sun yaki jam’iyyarsu a zaben shugaban kasa, Fayose ya ce ‘yan kungiyar G5 ba su da niyyar su sauya sheka daga PDP zuwa APC mai mulki.
A yayin da wanda ya fi kowa tsufa a tafiyar G5 ya kai shekara 62 a Duniya, jagoran na PDP a jihar Ekiti ya ce Samuel Ortom ya tsufa da ya tsallaka APC.
An rahoto Fayose ya na cewa ‘ya ‘yan Ortom za su rabu da shi idan a shekarunsa ya bar PDP, a game da Wike kuwa, ya ce ba zai taba canza sheka ba.
Ana bukatar irinsu Wike
Idan ya tashi kafa gwamnati, Fayose ya ce Shugaba Bola Tinubu ya na bukatar irinsu Nyesom Wike, ya ce ba zai ji dadi a jefar da shi duk da kokarinsa ba.
Tsohon Gwamnan ya sake nanata cewa bai bukatar zama Minista a gwamnati mai-ci, amma ya ce babu laifi idan aka ba Wike kujera a majalisar FEC.
"Ina so Wike ya shiga cikin gwamnatin nan. Wike yana da duk abin da ake bukata a bautawa Najeriya. Wike ya na da baki, kuma ya san kan aiki.
Najeriya na bukatar karamin shu’umi. Ina goyon bayan Wike. Idan Asiwaju ya ga cancantarsa ko wani daga cikin ‘Yan G5, su shiga gwamnatinsa."
- Ayo Fayose
Fayose: "Ina tare da APC a 2023"
Kamar yadda rahoto ya zo dazu, a tattaunawar ne aka ji tsohon Gwamnan ya ce APC ya yi wa aiki, kuma ya ba PDP shawarar ta daidaita al’amuranta.
Ayodele Fayose ya fadi dalilinsa na marawa Bola Tinubu baya kan Atiku Abubakar da PDP ta tsaida, daga ciki ya ce lokaci ya yi da mulki zai koma Kudu.
Asali: Legit.ng