Tinubu Nayi wa Aiki, Amma Ba Zan Karbi Tayin Minista ba – Tsohon Gwamnan PDP
- Ayodele Peter Fayose ya fito karara ya fadawa Duniya wanda ya goyi baya a zaben shugaban kasa
- Tsohon Gwamnan jigo ne a jam’iyyar PDP ba, amma yana tare da Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023
- Fayose ya ce Tinubu ya fi dacewa da mulki, ya yi alkawari ba zai karbi mukami a gwamnatinsa ba
Abuja - Ayodele Peter Fayose wanda ya yi Gwamna sau biyu a jihar Ekiti, ya shaida yadda ya taimaki Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023.
A maimakon ya goyi bayan ‘dan takaransu na PDP, Atiku Abubakar, Tribune ta ce Ayodele Fayose ya taimaki APC ne a takarar shugaban kasa.
Tsohon Gwamnan yake cewa jam’iyyar adawa ta PDP ba tayi masa adalci ba, saboda haka ya ki ba takarar Alhaji Atiku Abubakar gudumuwa.
Dalilan goyon bayan Tinubu
Babban jigon na PDP a Kudu maso yammacin Najeriya yake cewa Bola Tinubu ya dace a zaba domin bai kamata mulki ya tsaya a Arewa ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Fayose ya yi wannan bayani ne da aka yi hira da shi a kan sha’anin siyasar kasa a tashar talabijin nan na Channels a ranar Lahadin da ta wuce.
‘Dan siyasar ya shaida cewa duk da jam’iyyar APC mai mulki ya yi wa aiki a jihar Ekiti a zaben shugaban kasa, bai bukatar samun wani mukami.
Mun tsufa da neman mukami - Fayose
Idan har Tinubu ya tashi robon matsayi, Fayose yana ganin ya kamata ne a zakulo matasa.
“Ba na neman matsayi. Ba zan taba karba ba (yana nufin kujerar Ministan gwamnatin tarayya).
Idan ina so in fada maku gaskiya, duk wanda ya kai akalla shekara 65 a cikinmu, kamata ya yi Asiwaju ya fada mana mu je mu kawo ‘ya ‘yanmu.
Tun tuni an lalata masu makamo. Wasu sun lalata makomar wadannan yara masu tasowa.
-Ayo Fayose
Fayose ya ji haushi taba Joju
The Cable ta bibiyi hirar, ta ce Fayose ya ce ba zai taba goyon bayan jam’iyyar da ta dakatar da yaron cikinsa ba, duk da wahalar da ya yi da ita.
Bai taimaki PDP ba, Fayose ya ce ba za ta yiwu a goyi bayan Atiku da Tinubu a lokaci guda ba, sai ya zabi Bayaraben domin ana ganin darajarsa.
Za a binciki Gwamnatin baya
A makon jiya ne rahoto ya zo cewa Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila ya bijiro da batun jinginar da filin jirgin saman Kano da Abuja da aka yi.
Sannan za a binciki Dala $10m da gwamnatin Muhammadu Buhari ta kashe a aikin gas. Sanatoci sun ce kudin da kashe a kwangilar ya yi yawa.
Asali: Legit.ng