Gwamnan Sokoto Ya Tuka Kansa Zuwa Gidan Gwamnati Saboda Lattin Direbansa, Ya Gargadi Ma'aikata
- Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya yi gargadi ga ma'aikatan jihar da su rike aikinsu da muhimmanci don mutunta kansu
- Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake kokawa kan yadda ya tuko kansa a mota zuwa wurin aiki
- Gwamnan ya ce har karfe 8:30 na safe direbansa bai fito aiki ba, inda ya shiga ya tuka motar zuwa gidan gwamnati
Jihar Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya gargadi ma'akata da su dauki aikinsu da muhimmanci bayan samun matsalolin zuwa wurin aiki a latti a ranar Alhamis 6 ga watan Yuli.
Dalilin haka, gwamnan ya tuka mota da kansa har zuwa gidan gwamnati bayan ya jira direbansa har karfe 8:30 bai fito ba.
Bayan ya isa gidan gwamnati, ya fahimci ma'aikata da yawa ba su zo ba, sai ya umarci jami'an tsaro su rufe kofar shiga gidan gwamnatin don hana masu shigowa, Pulse ta tattaro.
Gwamnan ya bayyana yadda ya tuka kansa a mota saboda lattin direba
Ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Na tuna kaina har gidan gwamnati saboda direba na bai zo akan lokaci ba."
Mashigar gidan gwamnatin ta kasance a kulle har zuwa karfe 1:00 na rana.
Umarnin ya shafi manyan ma'aikata a gidan gwamnatin da ma su ba wa gwamnan shawara ta bangarori da dama, cewar rahotanni.
Ya gargadi ma'aikata da su rike aikinsu da muhimmanci
Ya kara da cewa:
"Wannan abin ba wasa ba ne, na yi alkawarin ba zanci amanar 'yan Sokoto ba ko kuma wani ma'aikaci ya ci amanar su.
"Ko mutum ya yi aiki ko kuma ya dawo da kudin da ya ci, ba za ka ci kudi ba tare da yin aiki ba."
Gwamnan bai bayyana matakin da zai dauka akan direbansa ko sauran ma'aikatan ba.
Tun bayan hawanshi karagar mulki, gwamnan ke alwashin kawo ci gaba a jihar.
Gwamna Ya Iske Mutum 3 Kadai Lokacin Da Ya Mamayi Masu Zuwa Aiki A Latti
A wani labarin, gwamnan jihar Sokoto, Aliyu Ahmed ya mamayi gidan gwamnati inda ya iske mutum uku kacal.
Ahmed Aliyu ya fita aiki ne a matsayin gwamna amma abin mamaki ma'aikata da dama ba su samu daman zuwa da wuri ba.
Gwamnan ya gargadi ma'aikata da su rike aikinsu da kyau ko kuma su dawo da kudaden da suka ci.
Asali: Legit.ng