Asalin Abin da Ya Kai Ni Wajen Tinubu a Aso Rock – ‘Dan Takaran Shugaban Kasa a PDP
- Anyim Pius Anyim ya ziyarci sabon Shugaban Najeriya a karon farko tun bayan rantsar da shi
- Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyar ya ce dalilinsa ziyararsa it ace taya Bola Tinubu murna
- Sanata Pium ya nemi tsayawa takarar Shugaban kasa a PDP a zaben 2023, amma bai samu tikiti ba
Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya yi zama Anyim Pius Anyim a ranar Laraba a fadar shugaban kasa, wannan sa-labule da aka yi ya bar mutane a duhu.
Punch ta ce Anyim Pius Anyim wanda yana cikin jagororin jam’iyyar PDP a Najeriya, ya yi bayanin dalilin yin zama da sabon shugaban kasar a fadarsa.
Da yake yi wa manema labarai bayani a jiya, Sanata Anyim Pius Anyim ya ce ba komai ya kawo shi wajen Bola Ahmed Tinubu ba illa taya shi murna.
Tsohon shugaban majalisar dattawan yake cewa ya taya Mai girma shugaban kasa murnar samun mulki da kuma nasarorin da ya fara samu a ofis.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Taya murna da karfafa gwiwa
‘Dan siyasar ya ce ziyararsa ta yi nufin karfafa gwiwa ne ga Tinubu wanda ya hau mulki a watan Mayu bayan karewar wa'adin Muhammadu Buhari.
“Babbar dama ce in samu ganawa da Shugaban kasa kuma in taya shi murna, da farko saboda rantar da shi a matsayin shugaban kasa na 16 a Najeriya
Sannan in kuma karfafe shi tare da taya shi murnar matakan da ya iya dauka zuwa yanzu.
Mun yi tattaunawar zuciya da zuciya, amma dai babban makasudin shi ne in taya shi murna.
- Anyim Pius Anyim
Olisa Metuh ya yabi Tinubu
Shi kuwa da Olisah Metuh yake magana, leadership ta rahoto shi ya na yabon Bola Tinubu, yana cewa gwamnatinsa ta nuna alamun hada kan al’umma.
A tsawon shekaru takwas da su ka shude, tsohon kakakin na PDP ya ce Najeriya ta shiga matsala, ya na mai sa ran sabuwar gwamnatin za ta kawo gyara.
Metuh wanda ya daina siyasar jam’iyya, ya kara da cewa babu manufofi da tsare-tsaren gwamnatin da za su yi nasara idan mutane ba su hadin-kai ba.
Nadin sababbin Ministoci
Wani rahoto da mu ka fitar ya nuna babu mamaki tsohon Gwamnan jihar Edo, Sanata Oserheimen Osunbor ya samu kujerar Minista a gwamnatin tarayya.
Kungiyar Elites Coalition for Good Governance ta kai wa George Akume sunayen mutanenta, daga ciki harda Adebayo Shittu da Amb. Musa Mohammed.
Asali: Legit.ng