Jerin Muhimman Takardun Da Tinubu Ya Gabatar A Kotun Zabe Don Kare Kansa Daga Atiku Da Obi
- Ana iya cewa aski ya zo gaban goshi a kotun sauraron karar zabe bayan Shugaba Tinubu ya fara kare kansa
- City Boy kamar yadda masoyansa ke kiransa, ya gabatar da takardu fiye da uku a matsayin hujja na kare kansa daga zargin da ake masa
- Shugaba Tinubu wanda a hukumance ya fara kare kansa a ranar Talata, 4 ga watan Yuli, ta hannun lauyansa Wole Olanipekun (SAN)
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Shugaba Ahmed Bola Tinubu da lauyoyinsa suna duk mai yiwuwa don ganin sun wanke kansu daga zargin da ake musu a kotun sauraron karar zabe.
A ranar Talata, 4 ga watan Yuli, Shugaban kasar ya fara kare kansa daga karar da Jam'iyyar Labour (LP) da dan takarar shugaban kasarta Peter Obi da Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) suka shigar.
Rahoto Na Musamman: An Bayyana Jihar Da Ka Iya Samar Da Ministan Kudi a Gwamnatin Shugaban Kasa Tinubu
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cikin awa 48 da suka gabata, Shugaba Tinubu, ta hannun lauyoyinsa, ya gabatar da jerin takardu a matsayin hujja don kare kansa daga zargin da abokan hammayarsa ke yi.
Ga jerin takardun da tawagar lauyoyin Shugaba Tinubu suka gabatar kawo yanzu
1. Takardun Karatu na Jami'ar Chicago
An dade ana cece-kuce kan batun takardar kammala karatu na Shugaba Tinubu gabanin zaben shugaban kasa na 2023.
Jam'iyyun adawa suna da shakku kan nagarta da ingancin takardun karatunsa na Jami'ar Jihar Chicago.
An gabatar da batun a matsayin korafi a gaban kotun zaben don tabbatar da soke takarar Tinubu.
2. Bizar Amurka ta Shugaba Tinubu
Kazalika, lauyan Tinubu, Wole Olanipekun (SAN), a ranar Talata, 4 ga watan Yuli, a yayin fara kare wanda ya ke wakilta, ya gabatar da bizar Amurka ta Shugaban Kasar.
Peter Obi Ya Shiga Cakwakiya Yayin Da Tinubu Da Shettima Suka Gabatar Da Wata Kwakkwarar Shaida a Kansa
Wannan kuma ya kunshi takardar samun gurbin karatu a Jami'ar ta Jihar Chicago.
3. Takardu daga Hukumar Shige da Fice
Kamar yadda Punch ta rahoto, Olanipekun ya kuma gabatar da takardu daga Hukumar Kula da Shige da Fice wato Immigration.
Takardun daga Immigration suna dauke da bayanai da ke nuna an amince Tinubu ya tafi Amurka tsakanin 2011 zuwa 2021.
4. Rahotanni da aka wallafa a jaridu
Lauyan na Tinubu kuma ya gabatar da labarai da rahotanni da aka wallafa a jaridu kan karar da kungiyoyi daban-daban suka shigar a kansa.
Kotun kuma ta karbi wasu tambayoyi da ake nema kotun ta warware su da Antoni Janar na jihohin Adamawa, Akwa Ibom, Bayelsa, Delta, Edo da Sokoto suka shigar a kotun koli, suna kallubalantar cancantar Tinubu na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Kotun wanda Mai Shari'a Haruna Tsammani, ke jagoranta ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar Laraba, 4 ga watan Yuli.
Shugaba Tinubu, APC da INEC Sun Fara Kare Kansu a Kotu
Tunda farko kun ji cewa Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai fara kare kansa daga zargin da Peter Obi da jam'iyyar Labour da Atiku Abubakar da PDP ke masa a kotun zabe a ranar Talata 4 ga watan Yuli.
A rahoton da BBC Pidgin ta fitar ya an rahoto cewa Hukumar Zabe INEC ta fara kare kanta tun kwana guda da ya gabata.
Asali: Legit.ng