Ministocin Tinubu: An Lissafo Sunayen Wike, Kwankwaso Da Sauransu Cikin Wadanda Za a Iya Zaba
- Wani sabon rahoto ya bayyana sunayen manyan yan siyasa da masu biyayya ga shugaban kasa Bola Tinubu da ke jerin ministoci
- Nyesom Wike, Rabiu Musa Kwankwaso, Farfesa Ishaq Olorode ko Isa Aremu, da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, da sauransu
- Ana iya sake zabar tsohon gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya
Manyan yan siyasa da dama da masu biyayya ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da fafutukar ganin sun samu shiga jerin ministocinsa na karshe.
Kamar yadda jaridar The Sun ta rahoto, jerin sunayen da aka tattara yana cike da yan tsohuwar jam'iyyar Action Congress of Nigeria (ACN) a kudu maso yamma.
Ana ganin wani shahararran dan siyasa, Prince Dayo Adeyeye, wanda ya kafa kungiyar SWAGA a 2023 shine ya yi nasarar samun mukamin daga jihar Eikiti.
An tattaro cewa tsohon gwamnan Osun, Gboyega Oyetola da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode sun samu shiga jerin sunayen domin wakiltan jihar kudu maso yamma.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An kuma tattaro cewa akwai yiwuwar a sake zabar Oyetola a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya.
Ana ganin Oyetola yana da damar samun wannan kujera saboda gogewarsa a bankin First Bank.
Tsohon dan takarar gwamna, Olusola Oke da Dr Tunji Abayomi suna fafatawa don samun mukamin minista da za a mikawa jihar Ondo.
Yankin arewa maso yamma
Akwai yiwuwar a zabi mataimakin shugaban jam'iyyar All Progressive Congress (APC) na kasa, Salihu Lukman, daga jihar Kaduna.
Ana kyautata zaton an rubuta sunan Rabiu Musa Kwankwaso yayin da Abdullahi Ganduje zai zabi wani da za a ba karin mukami daga jihar Kano.
Aliyu Magatakarda Wammako zai gabatar da wani ga jihar Sokoto yayin da Ahmed Sani Yarima zai yanke hukunci kan wanda za a zaba daga jihar Zamfara.
An tattaro cewa Ibrahim Masari, dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC na wucin gadi, yana zawarcin samun kujerar minista.
Ana kyautata zaton wani ma'aikacin gwamnatin tarayya daga jihar Jigawa zai samu kujerar jihar.
Tsohon gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, na iya kasancewa cikin jerin ministocin shugaban kasa Tinubu.
Yankin arewa maso gabas
An tattaro cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da gwamnan jihar Borno, Umara Zulum sun lamuncewa mataimakin shugaban APC na kasa a atrwa, Sanata Abubakar Kyari.
Dan takarar gwamnan APC, Sanata Emmanuel Bwatcha na iya samun mukamin minista daga jihar Taraba.
Tsohon gwamna, Malam Isa Yugudu da tsohon minista, Ali Pate na gwagwarmayar samun mukamin daga jihar Bauchi.
Ba karamin daaga ake sha ba a tsakanin Harouk Bamusa, Sanata Idris Umar da Jamilu Isiyaka Gwamna a jihar Gombe.
Ana ganin mijin Sanata Aisha Binani, Dr Ahmed Moddibo da babban jigon kungiyar kamfen din Cif MKO Abiola na 1993, Sanata Jonathan Zangwina na iya samun mukamin daga jihar Adamawa.
Rahoto Na Musamman: An Bayyana Jihar Da Ka Iya Samar Da Ministan Kudi a Gwamnatin Shugaban Kasa Tinubu
Arewa ta tsakiya
Ana ganin tikitin jihar Kwara zai rabu tsakanin shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Olorode ko Isa Aremu.
Tsohon sakataren gwamnatin jihar Neja kuma malami daga jami'ar Ibadan, Farfesa Yahaya Kuta, na iya samun mukamin a jihar Neja.
Ana iya fuskantar yar tangarda a jihar Nasarawa saboda baya ga shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu da Gwamna Abdullahi Sule, akwai wasu manyan yan takara biyu.
Ana ganin tsohon shugaban karamar hukuma kuma babban dan kashenin Tinubu, Musa Wayo da dan siyasa Labaran Magaji ma cikin wadanda ake ganin za su iya samun mukamin minista.
Babban sakataren gwamnatin tarayya, George Akume shine zai yanke hukunci a jihar Benue kuma Emmanuel Jime ne babban dan takara.
Akume da tsohon gwamna Joshua Dariye za su duba su samo wanda ya fi dacewa da kujerar a jihar Filato saboda gazawar tsohon gwamna Solom Lalong, a zaben da ya gabata.
Sai dai kuma, Lalong na kokarin ganin Yakubu Datti, tsohon kwamishinan jihar ya samu mukamin.
Gwamna Yahaya Bello zai zabi minista daga jihar Kogi.
Kudu maso gabas
Ana ganin tsohon sufeto janar na yan sanda, Mike Okiro, ne zai samu kujerar na jihar Imo.
Mataimakin shugaban APC na kasa, Emma Enekwu, na iya samun mukami daga jihar Enugu.
Ana ganin Andy Uba na iya samun mukamin a jihar Anambra saboda kusanta kansa da Tinubu yayin da ake ganin Uche Ukwunife na iya samun shigewa saboda jinsi.
Hasashe sun nuna shahararren ma'aikacin banki kuma mazaunin Lagas, Mac Wabara, na iya samun mukamin a jihar Abia.
Tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Sanata Dave Umahi, wanda ke cin moriyar alaka mai kyau da Tinubu shine zai zabi wanda zai hau mukamin a jihar.
Kudu maso kudu
Ko shakka babu tsogon gwamna Nyesom Wike zai samu mukamin minista a jihar Ribas a matsayin tukwicin aiki wajen nasarar shugaban kasa Tinubu.
Sanata John Onwah na iya samun mukamin daga jihar Cross River a matsayin dannan kirji saboda sadaukar da kudirinsa na takarar gwamna da ya yi wa Sanata Bassey Otu wanda ya yi nasara a zabe.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio zai gabatar da sunan wanda za a ba mukamin daga jihar Akwa Ibom.
Ana ganin tsohon manajan darakta na NDDC, Dan Abia, na cikin sauran manyan yan takara.
Babban sakataran jam'iyyar APC na kasa, Felix Morka, tsohon minista, Festus Keyamo da Frank Kokori za su yi fafutukar samun mukamin na jihar Delta.
Ana sa ran tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan zai marawa wanda aka zaba daga jihar Bayelsa kuma ana ganin wani Davekeme Ikwigwa yana cikin yan takarar.
An yarda cewa Sanata Adams Oshiomhole ne zai zabi wanda za a ba mukamin a jihar Edo domin taimakawa APC wajen yin maganin Gwamna Godwin Obaseki a zaben gwamnan jihar mai zuwa.
An tattaro cewa Shugaban kasa Tinubu na tattaunawa da Sanata Sidi Ali da Isa Rahma da manyan masu ruwa da tsaki kan yiwuwar ba babban birnin tarayya mukamin minista.
Ministan kudin Tinubu na iya fitowa daga jihar Lagas
A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Shugaban kasa Bola Tinubu yana tunanin zabo ministan kudi daga jihar Lagas.
Wani lauya mazaunin Lagas, Wale Adeagbo, ne ya sanar da haka a wata hira ta musamman da Legit.ng ta yi da shi.
Asali: Legit.ng