Shugaba Tinubu Na Ganawa Yanzu Haka da Jiga-Jigan PDP a Aso Villa

Shugaba Tinubu Na Ganawa Yanzu Haka da Jiga-Jigan PDP a Aso Villa

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi bakuncin tsohon shugaban majalisar dattawa, Chief Pius Anyim da Olisa Metuh a Villa
  • Manyan jiga-jigan biyu tsoffin sakatarorin watsa labaran PDP sun shiga ganawar sirri da shugaban kasan yanzu haka
  • Wannan gana wa na zuwa ne a lokacin da ake tsammanin shugaba Tinubu na dab da miƙa sunayen ministocinsa ga majalisa

FCT Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga ganawar sirri da wasu tsoffin jigan-jigan jam'iyyar PDP 2 a Aso Rock da ke birnin tarayya Abuja.

Vanguard ta rahoto cewa Tinubu na ganawa da tsohon shugaban majalisar dattawa, Chief Pius Anyim da tsohon kakakin PDP na ƙasa, Olisa Metuh a fadar shugaban kasa.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Na Ganawa Yanzu Haka da Jiga-Jigan PDP a Aso Villa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Mista Anyim da Metuh, waɗanda duk sun riƙe mukamin Sakataren watsa labaran PDP na ƙasa, sun isa fadar shugaban ƙasa da misalin ƙarfe 1:30 na rana kuma suka wuce kai tsaye zuwa ofishin Tinubu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Shugaban APC Na Ƙasa da Sakatare a Villa

Idan baku manta ba a kwanakin baya, Olisa Metuh, ya sanar da cewa ya yi ritaya daga siyasa kuma ya fice daga jam'iyyar PDP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wannan gana wa na zuwa ne a daidai lokacin da ake tsammanin shugaban ƙasa Tinubu na shirin miƙa sunayen Ministocinsa ga majalisar dattawa domin tantance wa.

Takaitaccen bayani kan Anyim da Metuh

Mista Anyim ya yi aiki a matsayin sakataren gwamnatin tarayya a zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Dakta Goodluck Ebele Jonathan. Ya kuma nemi tikitin takarar shugaban ƙasa a PDP.

Haka zalika Sanata Anyim ya yi aiki da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar Ebonyi lokacin babban zaɓen 2023 da ya gabata.

A ɗaya ɓangaren kuma, Olisa Metuh, ya sanar da yin murabus daga jam'iyyar PDP da kuma jingine siyasa baki ɗaya a watan Oktoba na shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Ministan Buhari a Villa, Yan Najeriya Sun Nuna Damuwa

Wannan ne karon farko da Metuh ya kai ziyara ofishin lamba ɗaya a Najeriya tun lokacin da tsohon shugaban ƙasa Jonathan ya sha kashi a zaɓen 2015.

Tsohon kakakin jam'iyyar PDP ya sha fama da tuhume-tuhumen cin hanci da rashawa a lokacin mulkin Muhammadu Buhari, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Tinubu Ya Dora Mun Alhakin Dawo Da Zaman Lafiya a Zamfara, Yerima

A wani labarin na daban kuma Sani Yerima ya ce shugaba Tinubu ya ɗora masa alhakin dawo da komai kan hanya da zaman lafiya a jihar Zamfara.

Tsohon Sanatan ya bayyana haka ne a Aso Villa jim kaɗan bayan ganawa da shugaba Tinubu ranar Litinin, 3 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262