Abba Ya Kara Bada Mukamai 10, Kwankwaso da Jigon APC Sun Shiga Gwamnati

Abba Ya Kara Bada Mukamai 10, Kwankwaso da Jigon APC Sun Shiga Gwamnati

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada masu bada shawara da shugabannin hukumomi a jihar Kano
  • Yusuf Imam Shuaibu da Sadiya Abdu Bichi za su ba Gwamna shawara kan harkokin matasa da mata
  • Hisham Habib ya na cikin jerin wadanda Abba Gida Gida ya ba mukami, zai rike gidan rediyon Kano

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - A ranar Talata, 4 ga watan Yuli 2023, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin wasu manyan mukamai a gwamnatinsa.

Mai girma Abba Kabir Yusuf ya nada wasu da za su shiga cikin masu bada shawarwari na musamman da kuma shugabannin hukumomi.

Mai taimakawa Gwamnan na jihar Kano a kafofin sadarwa na zamani, Salisu Yahaya Hotoro ya tabbatar da wannan labari a shafinsa na Facebook.

Abba Gida Gida
Gwamnan Kano, Abba Gida Gida Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Rahoton da aka samu daga tashar rediyon Nasara FM ya ce hukumomin KAROTA, REMASAB da rediyon Kano sun yi sababbin shugabanni.

Kara karanta wannan

‘Dan Kwankwasiyya Mai Goyon Bayan Rusau Ya Koma Salati, Rushe-Rushe Ya Zo Kan Shi

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An dauko Ogan Boye da Danzago

Cikin wadanda su ka samu mukami, Legit.ng Hausa ta fahimci akwai Yusuf Imam Shuaibu wanda aka fi sani da Ogan Boye a siyasar Kano.

Sanusi Sirajo Kwankwaso ya zama mai ba Abba Yusuf shawara a kan sha’anin siyasa.

Gwamna Abba ya nada daya daga cikin jagororin APC, Ahmadu Haruna Danzago a matsayin shugaban hukumar da ke kwashe shara a jihar.

Jerin wadanda aka ba mukamai

1. Injiniya Sulaiman Sani - Mai ba gwamna shawara kan noman rani da madatsun ruwa

2. Abdullahi Shuaibu - Mai ba gwamna shawara kan Asusun Fansho

3. Yusuf Imam Shuaibu - Mai ba gwamna shawara kan harkokin Matasa da Wasanni

4. Sadiya Abdu Bichi - Mai ba gwamna shawara kan harkokin Mata Yara Da Nakasassu

5. Dr Nura Jafar Shanono - Mai ba gwamna shawara kan Albarkatun Ruwa

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Ministan Buhari a Villa, Yan Najeriya Sun Nuna Damuwa

6. Sunusi Sirajo Kwankwaso Mai ba gwamna shawara kan lamuran siyasa

Sababbin Darektoci a hukumomi:

7. Injiniya Faisal Mahmud Kumbotso - KAROTA

8. Alhaji Abdullahi Rabiu - Hukumar harkar gidaje

9. Alhaji Ahmadu Haruna Danzago - Hukumar REMASAB

10. Hon Hisham Habib – Rediyon Kano

'Yan fansho sun samu hakkokinsu

Daf da bikin babbar sallah ne aka ji labari cewa Gwamnan jihar Kano da aka fi sani da Abba Gida Gida ya sa al’umma da-dama cikin farin ciki.

Bayan biyan kudin jarrabawa daliban sakadare a Kano, sabuwar Gwamnati ta biya albashi da kuma fansho ba tare da an zaftare ko sisin kobo ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng