Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC Ta Yi Fatali Da Jagororin Majalisa Da Aka Sanar
- Ga dukkan alamu sabon rikici na shirin ɓarkewa a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a ƙasar nan
- Hakan na zuwa ne bayan shugabannin majalisa ta 10 sun sanar da sunayen jagororin majalisar ba tare da sanin uwar jam'iyya ba
- Jam'iyyar a nata ɓangaren ta yi fatali da sunayen ƴan majalisar da aka sanar inda tace ba haka tsarin fitar da su yake ba
FCT, Abuja - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta nesanta kanta daga jagororin majalisa da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da kakakin da kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas suka sanar.
Shugabannin majalisar dai sun sanar da sabbin jagororin majalisar ne a zaman da aka gudanar ranar Talata, 4 ga watan Yuli.
Amma da yake jawabi ga gwamnonin jam'iyyar, Abdullahi Adamu, shugaban jam'iyyar na ƙasa, ya bayyana cewa jam'iyyar ba ta da hannu a cikin sunayen ƴan majalisar da aka sanar, cewar rahoton Daily Trust.
Adamu ya ce shi ma sai dai ya ji raɗe-raɗi na yawo a kafafen watsa labarai cewa an naɗa jagororin majalisar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Adamu bai san da cewa za a sanar da sunayen jagororin majalisar ba
Shugaban jam'iyyar ya ce duk da ya karɓi baƙuncin shugabannin majalisar lokacin da suka kai masa ziyara barka da Sallah a ƙarshen mako, bai san cewa za a sanar da sunayen jagororin majalisar ba.
A kalamansa:
"Amma yanzu kawai na ke ji a matsayin jita-jita a kafafen watsa labarai cewa an fitar da wasu sanarwoyi a majalisar dattawa da ta wakilai."
"Hedikwatar jam'iyyar APC ta ƙasa da kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) bai fitar da wannan bayanin ba ko sanar da zaɓin jagororin ba."
"Sannan har sai mun tattauna a tsakaninmu mun fitar sannan mu tura musu a rubuce wanda hakan shi ne abinda aka saba yi, ba mu da niyyar kaucewa daga wannan tsarin."
"Domin haka kowace irin sanarwa da shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa, kakakin majalisar wakilai ko mataimakinsa suka yi, ba daga gare mu bane."
Akpabio Ya Sanar Da Jagororin Majalisar Dattawa
A wani labarin kuma, shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio, ya sanar da jagororin majalisar dattawa ta 10 a ranar Talata, 4 ga watan Yuli.
Sanata Bamidele ya zama shugaban masu rinjaye na majalisar inda Sanata Dave Umahi ya zama mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar. Sanata Ali Ndume ya shiga cikin jagororin majalisar.
Asali: Legit.ng