Majalisa Ta 10: Abubuwa 12 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban Masu Rinjaye Opeyemi Bamidele

Majalisa Ta 10: Abubuwa 12 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban Masu Rinjaye Opeyemi Bamidele

Bayan tattake wuri kan neman manyan muƙamai a zauren Majalisar Dattawan Najeriya, an bayyana sunan Michael Opeyemi Bamidele a matsayin shugaban masu rinjaye na majalisar.

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ne ya bayyana sunan Bamidele da mataimakinsa a ranar Talata, lokacin da majalisar ta dawo daga hutun makonni uku da ta tafi.

Michael Opeyemi Bamidele ne shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa
An bayyana Michael Opeyemi Bamidele a matsayin shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa. Hoto: Michael Opeyemi Bamidele
Asali: Facebook

Michael Opeyemi Bamidele ɗan siyasa ne a matakin Majalisar Dattawa, wanda a halin yanzu yake wakiltar Ekiti ta tsakiya a majalisar ta tara.Michael Opeyemi Bamidele ɗan siyasa ne a matakin Majalisar Dattawa, wanda a halin yanzu yake wakiltar Ekiti ta tsakiya a majalisar ta tara.

Muhimman abubuwa 12 dangane da sabon shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa

1. An haifi Bamidele ne a garin Iyin Ekiti da ke jihar Ekiti a shekarar 1963. Sai dai Opeyemi ya girma ne a garin Legas, inda can ya gudanar da mafi yawancin rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Wike Ya Yi Gagarumar Nasara Kan Atiku Yayin Da Dan Takararsa Ya Samu Babbar Kujera a Majalisar Dokoki

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bamidele ya sha gwagwarmaya gami da riƙe manyan muƙamai da dama a jihar ta Legas.

2. Opeyemi Bamidele ya yi karatunsa na sakandire a makarantar sakandiren Baptist Academy da ke Obanikoro cikin birnin Legas.

3. Bayan kammala sakandire, Bamidele ya wuce zuwa jami'ar Obapemi Awolowo da ke Ile-Ife ta jihar Osun, inda ya yi digirinsa na farko a jami'ar.

4. Bayan kammala digirinsa a jami'ar Ile-Ife, ya wuce zuwa jami'ar Benin da ke jihar Edo, inda ya yi digiri a ɓangaren shari'a.

5. Har ila yau, Bamidele ya zarce zuwa jami'ar Franklin Pierce da ke ƙasar Amurka, inda ya yi digiri na biyu a ɓangaren shari'a.

6. A shekarar 1992, Bamidele ya shiga zaɓen fitar da gwani na neman takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Oshodi/Isolo da ke jihar Legas, a ƙarƙashin jam'iyyar SDP inda ya sha kashi hannun abokin karawarsa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tajudeen Abbas Ya Bayyana Sunayen Sabbin Jagororin Majalisar Wakilan Tarayya Ta 10

7. Michael Opeyemi Bamidele ya yi aiki da Bola Ahmed Tinubu lokacin da yake sanata, a matsayin mai taimaka masa kan harkokin shari'a.

8. A watan Yulin shekarar 2000, Tinubu ya naɗa Bamidele matsayin babban mataimaki na musamman kan harkokin siyasa da alaƙa tsakanin gwamnatoci a lokacin da yake gwamnan Legas.

9. A shekarar 2003, Tinubu ya naɗa Opeyemi kwamishinan matasa da wasanni da ci gaban zamantakewa na jihar Legas, muƙamin da ya riƙe har zuwa shekarar 2007.

10. A watan Afrilun 2011, an zabi Opeyemi a matsayin ɗan Majalisar Wakilai don ya wakilci Ekiti ta tsakiya ta ɗaya, a zauren Majalisar Wakilai ta bakwai.

11. Bamidele ya yi takara a zaɓen gwamna na jihar Ekiti da ya gudana a shekarar 2014 ƙarƙashin jam'iyyar Labour, sai dai Bamidele ya sha kashi hannun Ayo Fayose.

12. A shekarar 2019 ne aka zaɓi Bamidele a matsayin sanata da ke wakiltar Ekiti ta tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC Ta Fitar da Sanatoci, ‘Yan Majalisa da Za a Warewa Sauran Mukamai 8

Sanata ya faɗi yadda Ayu da Obi suka janyowa Atiku faduwa zaɓe

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan tsohon sanatan Enugu ta Kudu, Mathew Urhogide da ya bayyana cewa mutane biyu ne suka janyowa Atiku faɗuwa zaɓe.

Ya bayyana cewa rigimar Ayu da gwamnonin G5, da kuma ficewar Peter Obi daga PDP ne suka janyo sanadin faɗuwar Atiku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng