Kano: Kwankwaso Ya Yi Martani Kan Zargin Juya Abba Gida Gida, Ya Bayyana Yadda Ake Rokonsa Ya Rusa Gidaje

Kano: Kwankwaso Ya Yi Martani Kan Zargin Juya Abba Gida Gida, Ya Bayyana Yadda Ake Rokonsa Ya Rusa Gidaje

  • Jigo a jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya musanta zargin cewa shi yake juya gwamnatin Abba Gida Gida
  • Kwankwaso ya ce wannan rusau da ake magana, su a wurinsu gyara ne don haka ba wani abin tashin hankali ba ne
  • Ya bayyana yadda mutane suka rinka son a rusa gidajensu don a biya su diyya a lokacin mulkinsa a jihar

Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ya bayyana yadda mutane suke ta rokon shi ya rushe gidajensu a lokacin mulkinsa.

Ya karyata jita-jitar da ake yadawa na cewa shi yake juya gwamnatin Abba Gida Gida a jihar Kano da cewa wannan sharrin 'yan adawa ne.

Kwankwaso ya yi martani kan zargin juya Abba Gida Gida a Kano
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Jigon Jam'iyyar NNPP. Hoto: Hausa Legit.
Asali: Facebook

Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin hira da RFI Hausa a ranar Lahadi 2 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Allah Daya Gari Banban: Yadda Aka Sha Shagalin Bikin Wani Basarake Da Amaryarsa Kada

Kwankwaso ya karyata cewa shi yake juya Abba Gida Gida

Sanatan ya ce mutane suna bata lokacin su abin da jama'a suke so shi ne aiki a kasa, duka wannan makircin 'yan adawa ne, Daily Trust ta tattaro.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa:

"Wannan bata lokacin ku kuke yi, abin da talaka ya damu da shi ya gani a kasa, ko kai ne kake yi ko wane ne ya gani a kasa.
"Mu ai tawaga ce, kamu duk wannan hassada ce da kiyayya na 'yan hamayya da kuma 'yan jam'iyyar mu da suka yi kuskure suka saki layi, ai Ganduje ya yi gaban kansa kuma ya ci nasara."

Ya ce har rokonsa ake ya rusa gidaje don biyan diyya a lokacinsa

Da yake magana kan zargin ko shima ya bada filaye lokacin mulkinsa? Kwankwaso ya ce:

Kara karanta wannan

Dakyar na sha: Da jini na ya hau idan na fadi zaben sanata, tsohon shugaban APC ya magantu

"Lokacin da nake gwamna tsawon shekaru takwas ban taba ba da wani fili na makaranta tun daga firamare har zuwa manyan makarantu ba.
"Lokacin da muke fitar da layuka a Kano kamar wuraren Kwankwasiyya da Danladi Nasidi da Ibrahim Kunya da sauransu muna biyan diyya mai kauri.
"Da muka zo biyan diyya a 2011 na ce a duba nawa ake biyan diyya, aka duba na ce a ninka sau goma, mutane a garinnan sai da suka rinka neman ma muce zamu rushe gidajensu."

Kwankwaso Bai Fada Mana Komai Ba Kan Maganar Komawa APC, Buba Galadima

A wani labarin, jigo a jam'aiyyar NNPP, Buba Galadima ya ce Rabiu Kwakwaso bai ce musu komai ba akan komawarsa APC.

Galadima ya bayyana haka ne a wata hirarsa da 'yan jaridu a ranar Alhamis 29 ga watan Yuni.

Ya ce Kwankwaso ya shirya tsaf don yin aiki tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu don samun ci gaba a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.