Mamban PDP Ya Lissafo Dalilai Hudu Da Za Su Sanya Kotu Ta Kori Shugaba Tinubu
- Wani mamban jam'iyyar PDP ya nuna ƙwarin guiwarsa a Twitter cewa za a tabbatar da rashin cancantar Shugaba Tinubu a kotu
- Tinubu ya samu mafiya yawan ƙuri'u inda Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour Party ke biye da shi a baya
- Mamban na PDP ya lissafo dalilai huɗu da ka iya sanyawa a kori Tinubu da suka haɗa da zama ɗan ƙasar Guinea, bayar da kuɗi saboda laifi mai alaƙa da safarar ƙwaya da sauransu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wani mamba na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai suna Hon. Rilwan a Twitter, ya nuna ƙwarin guiwarsa kan cewa za a tabbatar da rashin cancantar Shugaba Tinubu.
Idan ba a manta ba dai hukumar shirya zaɓe ta INEC a ranae Laraba, 1 ga watan Maris ta bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Shugaban APC na Kasa Ya Yi Muhimmin Kira Ga Shugabannin Majalisa, Ya Bayyana Hanya 1 Da Za Su Taimaki Tinubu
Zaɓen shugaban ƙasa na 2023: Yadda Tinubu ya yi nasara akan Atiku, Obi - INEC
INEC ta sanar da cewa Tinubu ya lashe zaɓen shugaban ƙasa inda ya samu ƙuri'u 8,794,726.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai biye masa Atiku Abubakar, na jam'iyyar PDP ya samu ƙuri'u 6,984,520. Yayin da Peter Obi na jam'iyyar ya zo na uku da ƙuri'u 6,101,533.
Sai dai, Atiku da Obi suna ƙalubalantar sakamakon zaɓen a kotu. Dukkaninsu suna son kotu ta ƙwace nasarar Tinubu ta basu ko kuma ta soke zaɓen.
Dalilin da yasa za a tabbatar da rashin cancantar Tinubu - PDP
Rilwan, a wani rubutu da ya yi a Twitter, ya lissafo dalilai huɗu waɗanda za su sanya Tinubu ba zai iya kaucewa tabbatar da rashin cancantarsa ba.
Dalilan sun haɗa da:
1. Ya samu iznin zama ɗan ƙasar Guinea.
Jerin Jami'o'in Da Suka Kara Kudin Makaranta Tun Bayan Da Aka Sanya Hannu Kan Dokar Ba Dalibai Bashi
2. Ya bayar da $460,000 a dalilin laifukan da suka danganci safarar ƙwaya.
3. Bai bayyana wa INEC abubuwan nan guda biyu da aka lissafo a sama ba.
4. Ya bayar da satifiket na bogi daga jami'ar Chicago ga hukumar INEC
Abin lura anan shi ne dukkanin dalilan da mamban na PDP ya lissafo zargi ne kawai, wanda har yanzu kotu ba ta yi hukunci akai ba.
Omokri Ya Bayyana Bincikensa Kan Karatun Tinubu
A wani labarin kuma, tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya bayyana sakamakon binciken da ya yi kan karatun Shugaba Tinubu a jami'ar Chicago.
Reno Omokri ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya kammala karatunsa a jami'ar inda har lambobin girmamawa ya samu.
Asali: Legit.ng