Dan Takarar Gwamnan APC Ya Bayyana Yadda Aka Yi Masa Butulci Domin Tinubu Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa
- Ɗan takarar gwamnan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Oyo, Tesli m Folarin ya bayyana yadda zaɓen Tinubu ya shafe shi
- Folarin ya ce ya faɗi zaɓen gwamnan jihar ne saboda butulcin da aka yi masa domin Shugaba Tinubu ya lashe zaɓen shugaban ƙasa
- Folarin ya yi rashin nasara ne a hannun gwamna Seyi Makinde wanda yana cikin ƴan G-5 waɗanda suka marawa Tinubu baya a lokacin zaɓe
Jihar Oyo - Ɗan takarar gwamnan jihar Oyo a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen ranar 18 ga watan Mayu, Sanata Teslim Folarin, ya bayyana cewa butulci aka yi masa.
Folarin ya ce an yi masa butulcin ne a cikin ƙulla-ƙullar da aka kitsa domin jam'iyyar APC ta yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, Daily Trust ta yi rahoto.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda ya yi takara a zaɓen a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC, shi ne wanda ya yi nasara a zaɓen.
Jam'iyyar APC ce mafi girma a jihar Oyo, Folarin
Folarin ya bayyana cewa jam'iyyar APC ita ce jam'iyya mafi girma a jihar, domin ta lashe kujerun Sanatoci uku da kujerun ƴan majalisar wakilai tara cikin 14 da ake da su a jihar, cewar rahoton Tribune.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ɗan takarar gwamnan ya bayyana hakan ne a Idigbaro cikin yankin Ologuneru a birnin Ibadan, lokacin da yake jawabi ga magoya bayan jam'iyyar a wajen liyafar murna da aka shirya domin Hon. Remi Abasi Oseni, ɗan majalisa mai wakiltar Ibarapa/Ido a majalisar wakilai.
A kalamansa:
"Idan muna maganar jam'iyyar da ta fi girma a jihar Oyo a yau, jam'iyyar APC ce. Mun lashe kujerun Sanatoci uku, kujeru tara na ƴan majalisun wakilai. Za mu ƙara lashe wasu kujerun majalisar guda biyu saboda mutanenmu suna kotu. A ɓangaren zaɓen gwamna kuwa, butulci aka yi mana."
Ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya da suka ƙara haƙuri kan tsare-tsaren da Shugaba Tinubu ya fito da su, inda ya ce ya yi hakan ne domin ceto ƙasar nan daga halin da ta tsinci kanta a ciki.
Ba Zan Daina Ziyartar Shugaba Tinubu Ba, Gwamna Makinde
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya bayyana cewa ba za a daina ganinsa a Villa ba kai ziyara wajen Shugaba Tinubu.
Makinde ya ce zai ci gaba da zuwa wajen Shugaba Tinubu har sai ya samowa jiharsa abinda ya je nema a wajen shugaban ƙasan.
Asali: Legit.ng