Gwamnan Katsina Ya Fede Gaskiya, Ya Jero Abubuwan da ke Hana 'Yan Arewa Cigaba
- Dikko Umaru Radda ya alakanta matsalolin Arewa da rashin hadin-kai da samun jagora a yankin
- Gwamnan jihar Katsina ya na cikin masu ra’ayin cewa yawan yankin ya zama huhun ma'ahu
- Dr. Radda ya yabi Yarbawa da Inyamurai da ke Kudancin Najeriya, ya ce sun fi ‘Dan Arewa tsari
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Katsina - A wani bidiyo da ke yawo a kafofin sada zumunta na zamani, an ji Umaru Dikko Radda PhD ya na bayani kan rashin cigaban yankin Arewa.
A faifan da ya fito daga shafin Mahadi Shehu, an ji Dikko Radda ya na zargin son kai a matsayin abin da ya jawowa ‘Yan Arewacin Najeriya koma-baya.
Gwamnan jihar Katsina ya amsa tambaya ne a game da abin da ya zama tarnaki da dabaibayi ga yankin duk da adadin al’umma da yawan kuri’ar zabe.
Tashin hankali: Fitaccen malamin addini a Najeriya ya fadi a filin jirgin sama saboda tsananin rashin lafiya
Ta ina aka samu matsala?
“Hadin-kai ne, babu hadin-kai a Arewa, kowa shi kadai yake aiki. A Arewa kowa ta kan shi yake yi, babu wanda ya damu da ya al’umma za ta kasance.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kowa ta kan shi yake yi, babu shugabanci, babu wanda ya isa a ce shi kadai ne idan ya yi magana za a saurare shi a Arewar nan, don haka babu jagoranci.
Saboda haka abin da mu ke bukata shi ne jagoranci, girmama manya da kuma daukar matsaya da za ta yi aiki a kan duk wani mutumin da yake a Arewa.”
- Umaru Dikko Radda
Ayi koyi da Yarbawa da Ibo
Dikko Radda ya bada misali da Yarbawa wanda ya ce idan su ka tafi Landan ko wata kasar waje, sai sun zama silar jawo ‘yanuwansa zuwa kasashen ketare.
A lokacin da Bayarabe ya ke yi wa na shi hanyar samun alheri, Gwamnan ya ce akasin haka ne a Arewa, ya na mai fatan a nan gaba lamarin ya canza.
A cewar Radda, Inyamuran da ke zama a Arewacin Najeriya su na yaye yaran shagonsu da su ka dauko daga kauyensu, su ba su jari domin su kafu.
Gwamnan yake cewa a Arewa babu wani mutum ko tsari da yake taimakon al’umma, ya zargi shugabanni da kwadayi, ya ce a haka su ke saida mutanensu.
Sai dai ayi amfani da yawan yankin saboda siyasa, Dr. Radda ya ce a wasu lokuta manyan Arewa su kan ware saboda mukami ko samun abin Duniya.
Rikicin shugabanci a Majalisa
An saba cewa daga yankin Shugaban kasa ake samun shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, an samu labari wannan karo abin ya zo da sarkakiya.
Yawancin Shugaban yakin zaben wanda ya zama Shugaban majalisa yake samun kujerar, sai dai a yanzu ana kukan an yi watsi da 'Yan Arewa ta tsakiya.
Asali: Legit.ng