Sanata Basiru Ya Magantu Kan Rikicinsa Da Gwamna Adeleke Na Osun a Masallacin Idi
- A ranar Laraba ne aka samu hatsaniya tsakanin gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke da tsohon Sanata a jihar, Ajibola Basiru
- Hakan ya samo asali ne kan wurin zama a masallacin Idin, yayin da aka buƙaci sanatan ya tashi ya ba gwamnan wuri don ya zauna
- Sanatan ya shawarci gwamnan da ka da ya bari wasu da ba 'yan cikin gwamnatinsa ba su ɓata masa tafiya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Osun - Tsohon mai magana da yawun Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ajibola Basiru, ya caccaki gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, biyo bayan hatsaniyar da ta faru tsakaninsu a wajen sallar Idi.
Legit.ng ta kawo muku rahoto kan yadda aka samu hatsaniya a filin sallar Idi na Osogbo da ke jihar Osun, tsakanin jiga-jigan biyu na jam’iyyar PDP da na APC kan wurin zama.
Abinda ya faru tsakanin sanatan da Gwamna Adeleke a masallacin Idi
Sanata Basiru ya riga gwamnan zuwa masallacin Idin inda kuma ya zauna a sahun gaba tare da wasu manyan yan siyasa irinsu Cif Khamis Olatunde Badmus.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wani jigo a jam’iyyar PDP, Alhaji Muniru Raji, ya faɗawa Sanata Basiru cewa Gwamna Ademola Adeleke na kan hanyarsa ta zuwa masallacin Idin, inda ya nemi Sanatan da ya tashi daga wurin domin gwamnan ya zauna.
Sai dai Sanatan bai aminta da da ya tashi ba, wanda hakan ya janyo tada jijiyar wuya tsakanin magoya bayan ɓangarorin biyu, kamar yadda Daily Trust ta yi rahoto.
Wasu magoya bayan PDP da suka fusata, sun yi yunƙurin kai wa Sanata Basiru farmaki, sai dai sun fuskanci turjiya daga magoya bayansa.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna Adeleke, Mallam Olawale Rasheed ya fitar, ya bayyana lamarin a matsayin yunƙurin kashe gwamnan.
Martanin Sanata Basiru kan hatsaniyarsa da Gwamna Adeleke
Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan faruwar lamarin, Sanata Basiru ya shawarci Adeleke da cewa kada ya bari wasu da ba su shafi gwamnatinsa ba su karbe masa hidimar tsaronsa.
Sanata Basiru ya ƙara da cewa shi ya je masallaci ne domin ya gabatar da sallah ba domin siyasa ba.
Basiru ya ce ya riƙe muƙamin jiha na tsawon shekaru takwas, sannan a matakin ƙasa na tsawon shekaru hudu, idan gwamna ko wani babba zai halarci wani wuri, kamata ya yi a yi tsari yadda ya dace.
Wani ɓangare na kalamansa na cewa:
“Ba wanda zai ce ni ba na cikin manya a garin nan. Na yi wa’adi biyu matsayin kwamishina kuma na zama sanata a tarayyar Najeriya. Don haka ina so in shawarci gwamnan jihar Osun da ya kula wajen tafiyar da gwamnatinsa ta hanyar amfani da jami’an da suka dace wajen tsara al’amuransa.”
Sannan a hirarsa da gidan talabijin na Channels, Sanata Ajibola ya ce bai ga wani wuri da aka warewa gwamnan ba a lokacin da ya iso masallacin idin.
Peter Obi ya bai wa musulmi gudummawar kuɗaɗe don gyaran masallaci
Wani labari da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun karanta cewa, ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi, ya yi zama da wasu jagororin Musulmai a gidansa da ke jihar Anambra, jim kaɗan bayan idar da sallar Idi.
Peter Obi dai ga gayyaci jagororin Musulman ne zuwa gidansa domin taya su murnar sallah babba da aka gabatar a jiyar Laraba.
Asali: Legit.ng