Isa Pantami Ya Bayyana Kalubalen Da Ya Fuskanta A Lokacin Da Ya Ke Minista

Isa Pantami Ya Bayyana Kalubalen Da Ya Fuskanta A Lokacin Da Ya Ke Minista

  • Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin ƙasa na zamani , Farfesa Isa Ali Pantami, ya bayyana irin ƙalubalen da ya yi fama da su a ofis
  • Ya bayyana wasu siffofi guda 4 da ya ce muddun mutum na da ɗaya daga cikinsu ko duka huɗun, to dole ne ya yi matuƙar funskantar ƙalubale
  • Pantami ya ce tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya sha yaba masa kan ayyukan da ya gudanar

Makkah, Saudia Arabia - Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin dijital, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bayyana irin ƙalubalen da ya fuskanta a lokacin da ya ke minista.

Pantami ya zayyano wasu abubuwa guda huɗu da ya ce muddun kana da ɗaya daga cikinsu, za ka fuskanci ƙalubale mai yawa.

Ya yi bayanin ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Sunna TV a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya a ƙarshen makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Sokoto: An Yi Jana'izar Mahaucin da Jama'a Suka Kashe Bisa Zargin Ɓatanci Ga Annabi SAW, Shaidu Sun Bayyana Gaskiya

Pantami ya bayyana kalubalen da ya fuskanta a ofis
Pantami ya bayyana kalubalen da ya fuskanta a lokacin da yake minista. Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

Pantami ya ce nasarar da ya samu daga Allah take

Pantami ya ce duk wata nasara da ya samu a lokacin da yake ofis, ya sameta ne daga wurin Allah maɗaukakin sarki, inda ya ce tun da ya fara aiki, bai yi watsi da addu'a ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce baya gajiwa wajen yin addu'a a koda yaushe, haka nan ma yakan faɗawa 'yan uwa da abokan arziƙi cewa su taya shi da addu'a akan Allah ya ba shi ikon sauke nauyin da aka ɗora masa.

Pantami ya ce ba dole ba ne a samu wani daga cikin musulmai, da ya fuskanci irin ƙalubalen da ya fuskanta a yayin gudanar da ayyukansa.

Ya ƙara da cewa akwai wasu siffofi guda uku da in kana da ɗaya daga cikinsu, zaka fuskanci bin diddiƙi, yarfe, da ƙazafi musamman daga wasu daga jaridun kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Eid El Kabir: Portable Mai Wakar Zazu Ya Hargista Intanet Bayan Nuna Shanu 5 Da Raguna 2 Da Ya Siya Don Shagulgulan Sallah

Siffofin da Farfesa Isa Pantami ya bayyana sune;

1. Kasantuwarsa ɗan Arewa,

2. Hausa Fulani,

3. Kuma Musulmi, wanda ya ce ba zaka samu cikakken adalci ba daga irin waɗancan jaridun.

Pantami ya ce baya ga wadancan abubuwa guda uku da ya lissafo, akwai guda ɗaya da ya ƙara a kai, wanda kuma shi ne wanda aka fi tsana a cikinsu, shi ne zamansa

4. Malamin addinin Musulunci.

Ya kuma ce za a yi ta zuwa maka da abubuwa domin a ga ka yi baya-baya da addinin, ko kuma ka tauye shi, idan ba a samu haka ba sai a yi ta binka da abubuwa daban-daban.

A cewarsa:

“Kuma abinda ake sha'awa shi ne ka bar karantar da addinin, ni kuma na ce ba zan bari ba. Ba yadda ba a yi da ni ba, ni kuma na ce ba zan bari ba.”

Kara karanta wannan

NSA: Sabon Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaron Kasa Ya Kama Aiki Gadan-Gadan

Pantami ya ce Buhari ya sha yaba masa akan aikinsa

Pantami ya kuma bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sha yaba masa kan yadda yake gudanar da ayyukansa na ministan sadarwa.

Ya ce shugaban ya sha fada masa cewa ya gode sosai da riƙe amanar aikin da aka ba shi da yake yi.

Ministan Buhari ya samu wani aikin jim kaɗan bayan ajiye muƙami

A baya, Legit.ng ta kawo muku wani rahoto kan tsohon ministan yaɗa labarai, ƙarƙashin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, da ya samu aiki da wani kamfani na ƙasar waje.

Kamfanin mai suna Ballard Partners ne ya sanar da cewa Lai Mohammed ya zama ɗaya daga cikinsu a wata sanarwa da kamfanin ya fitar a shafinsa na Tuwita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng