Eid al-Adha: Atiku Abubakar Ya Taya Musulmai Murnar Sallah, Ya Nemi Babbar Alfarma 1 Daga Garesu
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya taya al’ummar Musulmai murnar bikin Eid-el-Kabir
- Alhaji Atiku Abubakar ya kuma buƙaci Musulmai da su yi wa Najeriya addu’a a filin Idi da za a yi gobe a sassan daban-daban na Najeriya
- Atiku ya ce Najeriya na buƙatar addu’o’i tare da ƙarfafa gwiwar Musulmai su yi koyi da sadaukarwar Annabi Ibrahim
Dan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya taya al’ummar Musulmi murnar bikin babbar sallah, wato Eid-el-Kabir.
Atiku ya kuma roƙi ‘yan Najeriya da su nemawa Najeriya samun albarka daga wurin Ubangiji domin ɗaukakata zuwa tafarkin zaman lafiya, kwanciyar hankali, da wadata, kamar yadda The Cable ta wallafa.
Atiku ya yi kira da Musulmai da su yi koyi da Annabi Ibrahim
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi wannan kiran ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 27 ga watan Yuni.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya bukaci Musulmai da su yi koyi da sadaukarwar Annabi Ibrahim ta hanyar kyautatawa ga mutanen da ke kewaye da su.
Atiku ya kara da cewa:
“Muhimmancin bikin Eid-el-Kabir ya shafi amfanin haƙuri da Ubangiji a cikin al’amuranmu a matsayinmu na 'yan adam, musamman ma da muke Musulmai”.
“Littattafan dukkan annabawan Allah suna cike ne da kyawawan misalai na yadda suka yi mu'amala da mutane a lokacin rayuwarsu.”
"An kuma umarce mu da mu bi tafarkin annabawa, musamman ma Annabi Muhammad (SAW), wanda ke nufin cewa dole ne mu gudanar da rayuwar yau da kullum a matsayin sadaukarwa, ba ga iyalanmu kaɗai ba, harma ga sauran mutanen da muke tare da su.”
Atiku ya yi kira ga Musulmi da su yi wa Najeriya addu’a
Dan takarar na PDP ya bukaci Musulmi da su yi wa Najeriya addu’a a filayen Sallar Idi daban-daban a faɗin kasar nan.
Eid El Kabir: Portable Mai Wakar Zazu Ya Hargista Intanet Bayan Nuna Shanu 5 Da Raguna 2 Da Ya Siya Don Shagulgulan Sallah
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma gargaɗi al’ummar musulmi da kada su yi almubazzaranci, sai dai su yi ƙoƙarin nuna farin cikin bikin ta hanyar taimakon mabuƙata.
A cewarsa:
“A halin yanzu Najeriya na buƙatar addu’a. Dole ne mu ci gaba da roƙon Allah Madaukakin Sarki da ya yi wa ƙasar nan albarka, ya kuma ɗaukaka ta zuwa ga tafarkin zaman lafiya, lumana, da wadata.”
Malamin addini ya gargaɗi Musulmi da kada su ci bashin rago don yin layya
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoton malamin addinin da ya gargaɗi al'ummar Musulmai da kada su ci bashin rago domin su yi layya.
Malam Muhammad Adewoyin ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Talata, a yayin da yake jawabi kan muhimmancin layya ga Musulmi.
Asali: Legit.ng