Siyasar Majalisa: Atiku Zai Tsinci Kan Shi a Sabon Rikici da ‘Yan G5 a Kan Tambuwal
- ‘Yan adawa su na da kujeru hudu idan an tashi rabon shugabannin majalisar dattawa da na wakilai
- Nyesom Wike da ‘Yan G5 su na da ‘yan takararsu, sun hada-kai da shugabannin APC a kan batun
- Atiku Abubakar da shugabannin PDP su na da wasu ‘yan majalisa dabam da su ke goyon baya
Abuja - Nyesom Wike da mutanensa da kuma Alhaji Atiku Abubakar za su sake fafatawa bisa dukkan alamu, bayan rikicin da su ka yi a zaben 2023.
A wani rahoto da aka samu daga This Day, an fahimci akwai rashin jituwa tsakanin jagororin jam’iyyar PDP game da siyasar majalisar tarayya a Najeriya.
Abin da ya jawo sabani shi ne yadda 'yan majalisu za su raba mukaman shugabannin marasa rinjaye. Atiku Abubakar da ‘Yan G5 su na nuna iko da jam’iyya.
Ana zargin Bola Tinubu ya na so a nada wadanda zai ji dadin aiki da su a matsayin shugabannin da za su kare hakkokin ‘yan jam’iyyar adawa a majalisa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Atiku Abubakar v G5
Jaridar ta ce ‘dan takaran shugaban kasa a PDP a zaben 2023 da kuma wasu shugabannin jam’iyya su na da ‘yan takararsu da su ke ganin sun dace.
A gefe guda, gwamnatin tarayya ta hada-kai da Nyesom Wike wanda jigo ne a jam’iyyar PDP domin ganin masu sassaucin adawa sun samu mukaman.
Alamu na nuna tsohon Gwamnan na jihar Ribas zai iya jagwalgwala lissafin da jam’iyyar PDP ta ke yi a majalisar wakilan tarayya da majalisar dattawa.
PDP na goyon bayan Tambuwal
Atiku Abubakar da jam’iyyarsa ta PDP su na so Sanata Aminu Waziri Tambawal ya zama shugaban marasa rinjaye, abin da Wike ba zai taba yarda da shi ba.
Punch ta ce ‘dan takarar G5 a wannan kujera shi ne Sanatan Kuros Riba ta Arewa, Jarigbe Jarigbe. Har yau tsohon Gwamnan bai tare da Aminu Tambuwal.
Saboda haka Wike ya yi zama da shugabannin majalisar a makon jiya domin ‘yan bangarensa su fito da shugabanni dabam da wadanda jam'iyya za ta tsaida.
Sauran wadanda su ke harin wannan kujera sun hada da Sanata Francis Fadahunsi, Abdul Ningi da Adamu Aliero daga jihohin Osun, Bauchi da kuma Kebbi.
A majalisar wakilan tarayya, rahoton ya ce Kingsley Chinda shi ne ‘dan takarar G5. Sai dai Bamidele Salam ya na neman zama shugaban marasa rinjayen.
An samu 'Yan G8 a Majalisar Dattawa
Rahoto ya nuna kujerar shugaban marasa rinjaye ta haddasa rigima tsakanin Sanatoci. Ana zargin APC da wasu jagororin adawa sun hada-kansu.
Aminu Tambuwal, Kawu Sumaila, Abba Moro da wasu Sanatoci biyar sun fitar da takarda, su na kukan za ayi wa ‘yan adawa karfa-karfa a zaben majalisa.
Asali: Legit.ng