Rikicin PDP: Wike Ya Kara Shiga Matsala Yayin Da Jam'iyyu 4 Suka Ayyana Yaki a Kansa
- Sanatocin jam'iyyu marasa rinaye a majalisar dattawa sun zargi tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike da ƙokarin ƙaƙaba musu shugabanni
- Sanatocin waɗanda suka fito daga jam'iyyu daban-daban sun haƙiƙance cewa za a samu shugaban marasa rinjaye ne ba tare da wani katsalandan ba
- A cewar wata sanarwa da jam'iyyun suka fitar a ranar Asabar, sun ce sun shirya yin yaƙi da tsohon gwamna Wike, jam'iyyun sun haɗa da PDP, NNPP, LP, da YPP
FCT, Abuja - Sanatocin ɓangaren marasa rinjaye sun shirya fafatawa da tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, bisa zargin shirin ƙaƙaba ɗan takararsa a matsayin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa.
An rahoto cewa aƙalla jam'iyyu huɗu ne da suka haɗa da Peoples Democratic Party (PDP), New Nigeria Peoples Party (NNPP), Labour Party (LP), da Young Progressives Party (YPP) suka shirya fito na fito da Wike.
Dalilin da ya sanya jam'iyyun adawa ke faɗa da Wike
A cewar rahoton, jam'iyyun guda huɗu sun sha alwashin tabbatar da cewa Wike bai samu nasara ba a wannan ƙudirin nasa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A halin da ake ciki yanzu tsohon gwamnan ba ya ɗasawa da wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP, waɗanda su ke zarginsa da kawo wa jam'iyyar tangarda a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.
Majiyoyi a cikin jam'iyyar PDP sun bayyana cewa masu adawa da Wike a jam'iyyar na kawo tangarɗa kan ƙoƙarin kawo sulhu da muƙaddashin shugaban jam'iyyar na ƙasa, Umar Damagum, yake yi.
PDP, Labour Party, da sauran jam'iyyu sun ayyana yaƙi kan Nyesom Wike
A cikin wata sanarwa da suka fitar a birnin tarayya Abuja a ranar Asabar, 24 ga watan Yuni, jam'iyyun na PDP, NNPP, LP, da YPP, sun bankaɗo shirin kawo ruɗani da ake yi a tsakaninsu domin kawo mulkin kama karya a majalisar.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Sanatocin jam'iyyu marasa rinjaye za su zauna bayan majalisa ta dawo zamanta, sannan tare da yin shawara da jam'uyyin mu, za mu zaɓi shugabannin mu ba tare da katsalandan ba daga marasa kishin dimokuraɗiyya a ciki ko a wajen majalisa."
An Fara Maganar.Dawowar Wike Jam'iyyar APC
A wani labarin kuma, wani daga cikin manyan ƙusoshin jam'iyyar APC a jihar Rivers, Cif Tony Okocha, ya bayyana cewa a shirye su ke su yi maraba da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike, zuwa cikin jam'iyyar.
Okocha ya ce gudunmawar da Wike ya bada a zaɓe Tinubu yakamata a ce sabuwar gwamnatin ta tafi tare da shi.
Asali: Legit.ng