Kotun Zaben Shugaban Kasa: Jerin Manyan Shaidun Da Atiku Ya Gabatar Kan Tinubu a Gaban Kotu Sun Bayyana
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya gabatar da shaidu akan Shugaba Bola Tinubu a gaban kotun zaɓe
- A cewar Atiku, "Tinubun da ya halarci jami'ar jihar Chicago" yana da bayanai waɗanda suka bambanta da na ɗan takarar jam'iyyar APC
- Shaidar da aka gabatar ta nuna "Tinubun da ya halarci jami'ar jihar Chicago" an haife shi ne a 1954 sannan ya gama makarantar Government College, Legas
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Bayanai na ta fitowa kan girman shaidun da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Atiku Abubakar, ya gabatar akan Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Atiku ya gabatar da shaidun ne a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa mai zamanta a birnin Tarayya Abuja ranar Juma'a, 23 ga watan Yunin 2023.
Kotun Zabe: APC Ta Shirya Kwace Kujerar Sanatan Kaduna Ta Tsakiya a Hannun PDP, Ta Gabatar Da Manyan Shaidu 6
Atiku ya gabatar da manyan shaidu akan Shugaba Tinubu
A cewar Demola Olarewaju, mai taimakawa Atiku na musamman kan harkokin watsa labarai, takardun da ɗan takarar na PDP ya gabatar sun nuna cewa "Tinubun da ya halarci jami'ar jihar Chicago an haife shi ne a 1954 ba 1952" kamar yadda Shugaba Tinubu yake iƙirari ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Olarewaju a shafinsa na Twitter mai suna @DemolaRewaju, ya ƙara da cewa "Tinubun da ya halarci jami'ar jihar Chicago" ɗan ƙasar Amurka ne (baƙar fata) yayin da a takardun da aka ba INEC, ɗan takarar na APC ya ce shi ɗan Najeriya ne kawai kuma bai taɓa samun hurumin zama ɗan wata ƙasar ba.
Ya kuma ƙara da cewa Tinubun da ya halarci jami'ar jihar Chicago ya kammala karatu ne a makarantar sakandiren Government College, Legas, a shekarar 1970, yayin da Shugaban ƙasa Tinubu ya kasa bayyana makarantar sakandiren da ya yi karatu.
Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Fasa Dawowa Gida Najeriya Daga Faransa, An Bayyana Inda Jirginsa Zai Shilla
Kotu Ta Amince Da Korafin Atiku Kan Shugaba Tinubu
A wani labarin kuma, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, na ƙara ganin haske a ƙarar da yake yin kan nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Haakn na zuwa ne bayan kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasar, ta amince da takardun shaidar da Atiku ya gabatar a gabanta, inda yake ƙalubalantar sahihancin takardun karatun Shugaba Tinubu.
Asali: Legit.ng