Nadin Ministoci: An Shawarci Tinubu Da Kar Ya Yi Kuskuren Nada Kai Da Buhari Ya Yi A Lokacinsa
- An shawarci Shugaba Bola Tinubu, da kar ya yi kuskuren naɗa kansa minista kamar yadda tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi
- Wani fitaccen lauya, Wale Adeagbo, ɗan garin Ibadan ne ya bayyana haka a yayin da yake tsokaci game da batun ministocin na Tinubu
- Ya ce yin haka ya saɓawa tanadin da kundin tsarin mulkin ƙasar nan ya yi, za a iya maka shi kotu a kuma yi nasara a kansa
Oyo - Wani masanin doka Wale Adeagbo, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da kar ya yarda ya bai wa kansa muƙamin minista kamar yadda tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi.
Adeagbo wanda ɗan asalin birnin Ibadan ne ya shaidawa Legit.ng cewa, dole ne Tinubu ya kiyaye aikata hakan don gudun karya dokar ƙasa.
Saɓa doka ne Tinubu ya naɗa kansa matsayin minista
Lauyan ya ce a shari'ance, kotu za ta iya ƙalubalantar Tinubu in ya aikata hakan, saboda doka ba ta ba da damar riƙe muƙamai biyu a lokaci ɗaya ba, wato muƙamin minista da na shugaban ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamansa:
“Duk wani abu da shugaban ƙasa zai yi yana nan ƙarsƙashin doka, idan ya aikata wani abu da ya saɓa da kundin tsarin mulki, to wannan abu ya taka doka kuma za a iya gabatar da shi gaban kotu, wacce zata iya dakatar da hakan.”
“Ya kamata mu tuna cewa ofishin shugaban ƙasa matsayi ne na zartaswa, sannan kuma ofishin minista ma muƙamin zartarwa ne kuma a bayyane yake a tsarin mulki cewa gwamna da shugaban ƙasa, bai kamata su riƙe wani mukami na zartaswa ba.”
Ku tuna cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya riƙe ministan man fetur na tsawon shekaru takwas. Adeagbo ya ce irin wannan tsari bai dace ba kuma ba daidai ba ne.
An buƙaci Tinubu ya sa a binciko Sanusi Lamido Sanusi
A baya Legit.ng ta kawo muku rahoto cewa an buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu ya binciki tsohon sarkin Kano kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Muhammadu Sanusi Lamido Sanusi.
Wani jigo a jam’iyyar APC, Kailani Muhammad ne ya yi roƙon, inda ya ce kamata ya yi a sanya Sanusi ya amsa wasu tambayoyi dangane da tsigesa da aka yi daga mukaminsa a baya.
Muhammad ya buƙaci shugaba Tinubu da ya daina saurarar Sanusi, inda ya kara da cewa ɗan neman suna ne kawai.
RMAFC ta musanta batun ƙarin albashin Tinubu da sauran 'yan siyasa
Legit.ng ta kawo muku rahoto kan Hukumar tattare kuɗaɗen shiga da kula da kasafin kudi (RMAFC), ta musanta labarin da ya karaɗe ko ina, na cewar ta ƙara yawan albashin shugaban ƙasa Tinubu, mataimakinsa Shettima, da ma na wasu manyan 'yan siyasa.
Hukumar ta hannun jami'inta na hulɗa da jama'a, Christian Nwachukwu, ta bayyana cewa har yanzu shugaban ƙasa bai kai ga amincewa da batun ba.
Asali: Legit.ng