Jigon APC Alhassan Yaryasa Ya Miƙa Wata Babbar Buƙatarsa Wurin Tinubu Dangane Da Abba Gida Gida

Jigon APC Alhassan Yaryasa Ya Miƙa Wata Babbar Buƙatarsa Wurin Tinubu Dangane Da Abba Gida Gida

  • Alhassan Yaryasa, jigo a jam'iyyar APC ta Kano, ya nemi Tinubu ya takawa Abba Gida Gida birki kan abubuwan da ke faruwa a jihar
  • Ya ce rushe-rushen da Abba yake yi a yanzu na da alaƙa da gabar da ke tsakaninsa da gwamnatin baya ta Abdullahi Ganduje
  • Ya ce bai kamata a zura ido a barsa yana ci gaba da ruguje ayyuka na maƙudan kuɗaɗe da aka yi don amfanin 'yan jihar ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Wani jigo a jam’iyyar APC a Kano, Alhassan Yaryasa, ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya yi gaggawar takawa Gwamna Abba Kabir Yusuf birki kan rusau ɗin da gwamnatinsa ke yi a faɗin jihar.

Yaryasa wanda tsohon kodineta ne na kungiyar yaƙin neman zaɓen Tinubu, ya yi kiran ne a wata tattaunawa da ya yi da jaridar The Punch a Kano ranar Talata.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba Ya Ɗau Zafi, Ya Umarci Dukkan Kwamishinonin da Ya Naɗa Su Bayyana Dukiya Nan Take

An nemi Tinubu ya sa baki kan rushe-rushen da Abba ke yi
Alhassan Yaryasa ya nemi Tinubu ya hana Abba ci gaba da rusau da taɓa masarautu. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Yaryasa ya faɗi dalilin rushe-rushen da Abba Gida Gida yake yi a Kano

Ya ce kiran ya zama wajibi don gudun kada al’amuran su ɗauki wani salo na daban, domin rusau ɗin ba komi bane illa gabar da ke tsakaninsa da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yaryasa ya kuma bayyana cewa rusau da gwamnatin NNPP ke yi, ya nuna karara cewa ta na son ruguje duk ayyukan da Ganduje ya yi ne kawai.

A cewarsa:

“Idan gwamnatin ta so, ta je ta rushe gadar sama da Ganduje ya gina, ko kuma ayyukan da ya karasa, waɗanda ya gada wurin Kwankwaso.”

Ya ce bai kamata a bari a ci gaba da rusa gine-ginen da aka yi da maƙudan kuɗaɗe ba don kawai sabuwar gwamnatin yanzu ba ta da kyakkyawar alaƙa da tsohuwar gwamnati.

Kara karanta wannan

Jigon PDP Bode George Zai Koma Wajen Tinubu a APC? Gaskiya Ta Bayyana

Ya nemi Tinubu ya hana Abba taɓa sabbin masarautun da Ganduje ya ƙirƙiro

Ya kuma yi kira ga shugaba Tinubu da ya shawarci gwamnan kan duk wani yunƙuri na taɓa sabbin masarautu da yake shirin yi, yana mai cewa duk wani yunkuri na rushe sabbin masarautan zai fuskanci turjiya daga talakawa.

A kalamansa:

“Ya kamata shugaba Tinubu ya ja kunnen Gwamna Abba Kabir Yusuf kan rusau ɗin da yake yi saboda illar da yake yi wa jihar ta fuskar tattalin arziƙi.”
"Ya kamata Tinubu kuma ya shawarci gwamnan kan shirinsa na rusa masarautu, saboda yin hakan ba zai yi wa jihar daɗi ba.”

Ya kuma yi kira ga Majalisar Dokokin ƙasar nan da ta samar da dokar da za ta hana ‘yan siyasa, musamman gwamnoni tsoma baki a harkokin masarautun gargajiya.

Abba Gida Gida ya tura sunayen kwamishinoninsa ga majalisar dokokin jihar Kano

Legit.ng a baya ta kawo muku labarin cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya aika da sunayen mutanen da yake so ya naɗa kwamishinoni a gwamnatinsa domin a tantancesu.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Yi Martani Mai Zafi Ga Wike Bisa Ikirarin Cewa An Sanya Masa Guba a Sakatariyar PDP

Abba dai ya turawa majalisar dokokin jihar Kano sunayen mutane 19 da yake so ya bai wa muƙamin kwamishinonin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng