Tuna Baya: Arangamar Abba da Matar Shugaban DSS, Yusuf Bichi Kafin Zama Gwamna

Tuna Baya: Arangamar Abba da Matar Shugaban DSS, Yusuf Bichi Kafin Zama Gwamna

  • Abba Kabir Yusuf ya tuno da takkadamarsa da Aisha Yusuf Bichi a filin jirgi a farkon shekarar nan
  • Abba Gida gida ya zargi matar Shugaban hukumar ta DSS da zaginsa da ci masa zarafi haka kurum
  • A lokacin ya na ‘Dan takarar Gwamna, ‘Dan siyasar ya ce an ce ba za a bar shi ya samu mulki ba
  • Watanni bayan wannan abu sai ga shi Abba ya zama gwamna, Yusuf Bichi ya bar kujerar hukumar DSS

Kano - Abba Kabir Yusuf ya fito ya fayyace abin da ya wakana tsakaninsa matar shugaban hukumar DSS, Aisha Yusuf Bichi a farkon shekarar 2023.

Legit.ng Hausa ta tuno cewa watanni da wannan sabani ne sai aka ji Yusuf Bichi ya bar kujerar da yake kai a DSS, shugaban kasa ya nada Adeola Ajayi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya yiwa fitaccen mawakin siyasa kyautar sabuwar mota, ya saki bidiyo

Mai girma Gwamnan ya yi amfani da damar wajen bada labarin bangarensa na sabanin da ya samu da mai dakin Yusuf Magaji Bichi a filin jirgi.

Abba Gida Gida da Matar Shugaban DSS
Abba Gida Gida da Matar DG DSS Hoto: /thunderblowers.com, @KYusufAbba
Asali: UGC

A bidiyon da aka wallafa a shafin tashar Rahma, an ji Abba Kabir Yusuf yana cewa Hajiya Aisha Bichi ce ta auka masa da zagi babu gaira babu dalili.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba Gida Gida ya zargi matar shugaban hukumar tsaron da zagin iyayensa har da yi masa barazanar cewa ba zai yi mulki ba, a yau shi ne Gwamna.

Haduwar matar Yusuf Bichi da Abba Gida Gida

A cewar Abba, tun farko ya je wajen matar ne domin ya fada mata abin da yaranta ke yi, mikewarta ke da wuya, ya ce sai ta zarge shi da rashin kunya.

Ko da ya samu sabani da Aisha Bichi, Gwamna Abba ya nuna akwai kyakkyawar alaka tsakaninsa da mai gidanta wanda shi ne ke rike da DSS.

Kara karanta wannan

Ana zargin rigima da Ribadu ya tilasta Bichi yin murabus daga shugabancin DSS

Ganin ya san mai gidanta, sai ‘dan takaran na NNPP (a lokacin) ya nemi tuntubar shi domin sanar da shi abin da ya faru, amma bai same shi a salula ba.

Sai aka fara ruwan zage-zage

A bidiyon, an ji Abba Yusuf ya na cewa daga nan sai wannan mata ta kira sunansa, ta rika zagin iyayensa, har abin ya kai aka hana shi shiga jirgin saman.

Baya ga haka, an gwabje wani da ke daukar hoto kuma aka yi yunkurin cafke ‘dan siyasar. Wani cikin 'ya 'yan shugaban jami'an tsaron ya karyata wannan.

"Wallahi ba za mu ba ka Gwamnan Kano ba, banza mai bakin jini. Ta gama zagin uwa ta da uba na. Uba na ya na kabari."

- Abba Kabir Yusuf

Abba: "Malamai su rika yin adalci"

Duk abubuwan da su ka faru a nan, Gwamnan Kano ya ce malamai ba su san an yi ba.

Kara karanta wannan

"Zan tsaya da kafafuna": Dan takarar gwamnan PDP ya sha alwashi, ya bugi kirji

Ba tare da kama suna ba, Gwamnan ya tunawa malaman Kano yadda wani daga cikinsu ya rika sharhi kan lamarin alhali bai saurari bangaren shi ba.

'Dan Gwamnan Kano ya samu mukami

An ji labarin cewa duk da Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin koyi da uban gidansa, Rabiu Kwankwaso na nesanta iyalinsa da mulki, bai iya cikawa ba.

Gwamnan Kano ya dauko wanda tamkar ‘da yake a wurinsa, Ahmad Abba Yusuf ya ba shi mukamin Sakataren hukumar da ke kula da tarihi da al’adu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng